KALUBALE BOOK 1

Page 10

by @yargidanimam

Muhseen ya dauke kallonsa daga gareta, yace 'Irin wanna kalion da ki ke min, shi ke haddasa min muzanta tare da fargaba domin tabbas in dai ki kal min Irin wannan kallon, na san ki na da wata babbar bukata wacce ni kadaine zan iya biya miki ita,, kin san kuma ba na jure bijire ma bukatarki komai nauyinta ko da ni zan cutu dole na biya miki bukatarki “.

Hajiya Goggo ta ginjina kai kaunar Muhseen ta kara kama zuciyarta, tace a sanyaye "Magajin Malam, sanin kanka ne, kai ne sanyin Idaniyarmu ni da Mallam, Muna yi maka son da mu kanmu ba zamu lya kwatantawa ba, kada ka manta, tun ka na da shekaru uku a duniya, rikonka da kula da rayuwarka ta dawo hannunmu, don me ko zai sa ba zamu jika a jikinmu da zuclyarmu ba? A rayuwata ba na son na ji laifinka komai Kankantarsa , burina kuma ace ka zama dan kwaral, fiye da duk ya'yan duniya. Magajin Malam, na san kai ma ko ba'a fada ba, ka damu, da maganar yin aurenka da ta zama abin tattaunawa a ko yaushe. Kowa yana neman dalilin da zai ci zarafinka a kan wannan maganar amma ina bukatar ka nuna mana damuwar taka a fili, ta hanyar ba kowa mamaki, ka amince da abinda muka zartar a kanka wanda kafin na zo nan sai da naje mu kayi magana da mallam,duk kuma mun tsaya akan magana daya ne, wanda nasan ba zaka taba bamu kunya ba” Muhseen ya kudundune Idanusa yace "Hajiya don Allah kada ki gabatar min da bukatar da za ta yi tsauri a gareni". Hajiya Goggo ta girgiza kal tace "Don Allah menene abin kin ka da aure? Menene damuwarka akan hakan? Ka yi girma, ka kai munzalin da zaka aje iyali , Me yasa kake son ka bata kuruciyarka?” Idanun Muhseen suka kara cika da hawaye, tamkar ba shine Wannan dakakken namijin da 'yan mata da yawa ke wawasonsa ba, yace cikin matukar sanyin jiki “Hajiya ba na kin aure, kuma ban rasa matan da suke sona ba sai dal matsalata da damuwata daya ce." Hajiya ta matso sosai kusa da shi tace “Yauwa, maza ka sanar da ni , dama na san ba-ka rasa wata matsalar, gaya min, ka ji? Muhseen ya numfasa gami da lankwashe hannayen sa biyu yace 'Wannan matsala tawa, ban taba gayawa kowa ba na barshi a cikin zuciyata duk da wahalar da hakan ke bani don gani nake wannan matsalar tawa tamkar almara ce kuma ba kowa zai yarda da abinda zan fada ba shi yasa na zabi yin shuru” ya kara gyara zamansa, a yayinda Hajiya Gwaggo ta kara zuba masa ido, alamar ta kosa ta ji abinda bakinsa zai furta, wanda kila shine karshen duk wannan badakalar. Muhseen ya cigaba da cewa , “tun lokacin dana kai munzalin aure. Gaba daya sal Allah ya zare min son kowa ce 'ya mace. Na tsani kowa ce 'ya mace da za ta ce Tana sona, saboda a duk lokacin da hakan ya faru nakan samu kaina cikin tsananin damuwa” ya dubi Hajiya Gwaggo sosai yace, “ kin san dalili ?” Ta yi saurin girgiza kai tace “ Aa” ya numfasa sannan yace “Duk a dalilin son wata da nake yi wacce ban santa ba ban san inda take ba, asalima ban taba ganinta ba." Hallya Goggo tayi zillo cike da fargaba tace 'Son wacce ba-ka sani ba? Wace irin magana ce wannan? “ Akaro na farko yay dan murmushi, yace “Wata kila ba zaki yarda da abinda zan fada ba wataklla kuma ki yi tunanin ina son na kauda tunaninku ne akan auren nawa , dalilin da yasa kenan kuma tun farko, na boye damuwata naki gaya ma kowa, nayi ta dakon damuwata ni kadai ina shan wahalata ni kadai,zuciyata na zafi kullum ni kadai nasan abinda nake ji a cikin zuciyata da jikiina ,