KALUBALE BOOK 1

Page 11

by @yargidanimam

Dole tasa na aje wannan sirrin ban gaya ma kowa ba, domin ina ganin tamkar za'a daukeni zautacce, ko makaryacl." Ya dan numfasa, lokacl daya ya maida kallonsa kan fuskarta, ya cl-gaha da cewa: "Tun lokacin da na yi girma, na mallaki hankalin kaina, da zaran na kwanta barcl, sal na yi mafarkin wata yarinya, wacce Idanunta kawai nake gani, ban taba ganin fuskarta ba, kuma kullum a cikin wani katon rami nake ganinta tana miko min hannunta. Ni kuma kullum cikin kokarin na kamo hannunta na fitar da ita daga cikin ramin nake. Amma hakan ya faskara. Hajiya kusan kullum sai na yi Irin wannan mafarkin, to da wannan yarinyar nake soyayya, ita nake masifar so. Ita nake kwadayin aure. Hajiya Ita ce ta kwace dukkan soyayyata. Shin Hajlya menene wannan, almara ce ko hauka ce, don Allah ki fahimtar da ni? Hajiya Goggo ta shiga salati, tana yin duk addu'ar da ta zo daga bakinta, sannan tasa hannu ta rike hannun Muhseen kam! Tana kare ma cikin idanunsa kallo tace a kidime "Haba al'amarinka dama na san ai ba banza ba, da walakin, wai goro a cikin miya, ka hadu da aljana Magajin Malam. Aljana ce ta aureka, shi yasa ba- ka son aure Inna-lillahl'wa'Inna-llaihir-rajl'un! Muhseen ya girgiza kai , lokaci daya gami da mikewa tsaye ko’ina a jikinta rawa yake yi , ya cigaba da kallonta yace "Ba aljana bace Hajiya, haka nake Ji a jikina." Ido ta bl-shi da shi, har ya mike shiga dakinsa, ya bude jakarsa ya fito da takarda, ya fito har yanzu hangame take da baki. Ya mika mata takardar "Hajiya duba ki gani, da kaina na zana Idanun nata da nake gani a mafarkina." A hanzarce ta amsa, ta bude ta kura ma kyawawan Idanun, idanu, idanu ne masu matukar kyau, tamkar tana jIn barcl dara-dara da gashin saman ido zara-zara. Hajiya Goggo ta numfasa tace 'Haba Magajin Malam, daga ganin wadannan kyawawan idanun, ai ka san aljanu ne. Aljanu sun riga sun shafeka, dole na sanarwa da Mallam, domin a san abin yi, kana cikin lalura, me yasa ka yi nawar sanar damu damuwarka. Ai damuwar mu ce mu ma." Muhseen ya girgiza kal yace 'Hajlya ki bar wannan maganar, kada ki damu kanki don Allah"., ta dube shi a hargitse tace 'Ya za'ayi na bar wannan