Page 12
maganar? Al ba za ta yuwu ba ya zama dole mallam ya ji wannan mayanar domin ya taikaka maka ." Ya tsura mata ido, a yayin da ta ci- gaba da cewa "Bukatanu a yanzu shine ka auri Haneefa, don haka dole na gaya ma Malam a samu a raba-ka da aljanar, domin mu samu ka kaunaci "yar-uwarka ka kuma aureta. Haneefa ita ce zabin da muka yi maka yarda da shi, kayi hakuri ka karbeta ka aureta komai ya wuce." Kan Muhseen yayi nauryl yace "Hajlya ba na son Haneefa, bata kwanta min a rai ba dabi’unta da tsarinta duk basu yi min ba". Tace "Ba komal, tunda ba ita kadai bace, ba-ka so, duk 'yan matan duniya ne ba-ka so. Ba damuwa Haneefa zayi hakuri da kai domin yanzu ne na kara tabbatar da cewa itace ta dace da kai domin itace dolenka itace zata Iya jure koma meye." Muhseen bai kara magana ba, har Hajiya Goggo ta tashl, jikinta na rawa duk ta rude tace 'Zan je na sami Malam ka kwanta ka huta, kafin ya nemeka." Kal kawai ya gyada, ta dauki tiren abincin ta fita a sukwane. Muhseen ya mika hannu, ya dauko takardarsa, ya kura ma kyawawan idanun jiki Ido, tsigar jikinsa har tashi take, tamkar ana kara fisgar kaunarta cikin zuclyarsa. Shin wane Irin soyayya ne wannan? Son wanda ba-ka sani ba. Yau dai ya bude sirrinsa da yake damunsa. Muhseen mutam ne me ji da kai , miskilanci da kuma tsananin kauda kal akan komai,koda akan abinda ya dame shi ne, amma tunda ga fara fuskantar wannan al'amarin, rayuwarsa ta canja shi kansa yana son yayi aure, ko don ya faranta ma mahaifansa da kakanninsa da 'Yan-uwansa rai . Ya kuma tsira daga surutan jama'a'a a kansa. Bayan Muhseen ya idar da sallar issha'l, yana saman sallayarsa yana addu'a da hannayensa blyu a sama dai-dai lokacin Haneefa tayi sallama tana sanye cikin riga da wando, na wani farin (Material) me kyau, sal kamshl take yi, ta sami waje ta zauna tana jiran ya karasa addu'ar. Lokaci daya tana kare ma falon nasa Kallo rabonta da ta shigo, tun ranar sallah da suka zo ita da sauran 'Yan-uwanta, ya ba su barka da sallah.domin kuwa ba wani sakewa suke yi a gabansa ba.Yana Idar da addu'ar, ya juyo yana kallonta, ita ma idonta kyar! A kansa tana dan murmushi "Sannu da zuwa Babban Yaya." A dakile ya amsa "Yauwa, ya aka yi? Haneefa tace "Dama Hajiya Goggo ce tace na kiraka." Ya dauke kansa yace 'KI ce mata