Page 13
gani nan zuwa." Ta amsa da "To." Lokaci daya ta tashi. Sannu a hankali cikin rausaya jan hankali ta fice, ya numfasa "Lalle da gaske suke mutanan nan." Ya fada a fill, domin baya raba daya blyu, saboda shi Haneefa ta zo gidan. Lalle ko goben nan zan tattara na bar muku garinku," Ya fada a fill, yana kokarin tashi ya fita. Cikin karfin guiwa. A falon Sheik Sadisu ya sami Hajlya Goggo yana shigowa. Sheik yayi saurin mika masa hannunsa, ya kama ya janyo shi, ya zaunar da shi kusa da shi sosai yana kallonsa. Minti uku tsakani. Shelk Sadisu yace 'Magajin Mallam". Ya amsa "Na'am Malam." Ya Gyara zaman gilashin idonsa , yace 'Me yasa ba-ka gaya mana abinda ke damunka ba, tun farko sai da ka bari abu yayi nisa haka? Ya girgiza kal yace "Ina tunanin tamkar ba za ku gasgatani bane." "Me zai sa ka ce haka, me zai sa ba zamu "gasgataka ba? Ban ji dadin hakan ba." "Ka yi hakuri Malam." Ya dafa shi yace "Ba komai, babu abinda zai gagara ka kwantar da hankalinka “, ya kara kallonsa yace “ka na yin addu'a kuwa?” Muhseen yace 'Ka san ni Malam, ina yin addu'a sosai, ba dare ba rana, ba na yin sake da addu'a, domin na san addu'ar ita ke rike da mu a yanzu. Sheik yace "Na san haka, tun kana yaronka, don haka nake shakkar anya aljanu ne suka shafeka? Domin matukar ka na addu'a, aljani ba zai taba iya cutar da kai ba a rayuwarka. Ba ma aljani ba. Kowa ma, don haka nake wasi-wasin hakan." Muhseen ya ji dadin maganar Sheik, don haka yace 'Ni kaina jikina bai ba ni cewa aljana bace”. "Kana da shaidar hakan? Hajlya Goggo ta tambaye shi, tana kokarin hada ido da shi ya juya ya dubeeta yace 'Eh, domin a duk lokacin da na yi Isitihara akan Allah ya nuna min matar da zan aura, wadannan Idanun kawal nake gani." Sheik yace "A'a, to wannan wane irin al'amari ne? Kodayake Allah yana nuna Ikonsa ta inda duk ya ga dama, wannan ba abin Mamaki bane. Ubangiji shi kadai ya san abinda yake nufi",Hajya Goggo tace cikin rashin gamsuwa da maganganunsu "Mallam don Allah kada ka daka ta Magajin Mallam, tunda Allah ya hore maka sani to ka duba ka gani, a tabbatar da abinda ke damunsa, domin dai wannan aikin aljanu ne”. Ta karasa magana fuskarta na fitar da asalin tashin hankali.
Ku dakace ni
Daga taskar ✍🏻
Yar gidan imam KALUBALE BOOK 1 2009 Tsohuwar Ajiya Daga Habiba Abubakar Imam (Mrs Aliyu Mayere)
Bismillahir Rahma Nirrahim