Page 14
Sheik Sadisu yace 'Eh, ke ma kin kawo shawara, kuma da ikon Allah yau zan gabatar da wata Istihara, domin a tabbatar da abinda ke akwai saboda a san ta inda za’a fara" Ta injIna kai cike da damuwa tace "Allah ya taimaka, amma har yaushe mutum kamarka za ka zauna ba aure, ba kuma tunanin yl, al ba zal yuwu ba, lokaci baya jiran kowa. Sal dal mu mu jira shi". Sheik Sadisu ya kara tura gilashinsa sosai sannan yace "Tunda yanzu an gano matsalar, ai duk da saukl, kuma maganar Haneefa ka sa a ranka ita Allah ya zaba maka, domin kasan halin mita da ruko irin na sa’a , yanzu ta juya maganar tace ba’a sonta ne shi yasa aka ki amincewa da auren na ka da Haneefa , saboda haka kayi hakuri ina ganin babu wata matsala, haka za ka daure ka saurareta, kafin Allah ya tabbatar da auranku In sha-Allahu, ka rabu da wannnan matsalar." Muhseen ya dago da sauri ya dube shi, idanunsa cike da damuwa yace "Mallam ka na nufin daga kai har Hajiya kun amince da wannan hadin na Goggo Sa'a?” Sheik Sadisu yayi dan murmurshi gami da dubansa yace "Muhseen ka yi hakuri, da kai da Haneefa duk daya ne a gareni, amma sanin kanka ne na fifitaka fiye da duk jikokina, don haka ba na son na yi maka dole ko na tursasaka. Yin abinda ba-ka so. Amma babu yadda zan yi ba zan iya Jure Jin mugayen maganganu a kanka ba. Don haka ka yi hakuri ka amince da Haneefa jininka wacce nasan Zata iya jure zama da kai a cukin ko wane irin hali ka tsinci kanka ,kuma ta rufa maka asiri”
Muhseen dai yayi shiru, zuciyarsa na tafasa,komai ya tsaya masa hakanan gabansa yake dakan uku uku. Ya auri Haneefa yarinyar da bai taba jin ta a cikin zuciyarsa ba har Sheik Sadisu ya ci-gaha da cewa "Da kuma na ji matsalar ka yanzu ne na kara tabbatar da cewa Haneefa ce kawai ta dace ka aureta, domin Ita ce kadai za ta jure zama da kai a matsayinka na dan’uwanta" Ya juyo yana kallon Muhaseen, ganin yadda fukarsa ta sauya yasa Sheik yace "'Amma ba na son ka dami kanka, ka sami lokacl ka yi tunani sosai akan wannan maganar, zan saurareka har zuwa taro na gaba, nan da watanni biyu, babu kuma abinda za mu zartar har sai na ¡l inda tunaninka ya tsaya. Amma lalle ina son ace taro na gaba, ace ka amine da batun auran, domin ba zan jure jin maganganun 'yan’uwanka a kanka ba, ka ji Magajina? Wannan maganar ta Sheik ita kadai ce ta dan sanyayar ma da Muhseen zuciya ta kuma rage radadin da take masa, yace yana kallon fuskar Sheik sadisu "Nagode mallam Allah ya kara lafiya da nisan kwana” sheik sadisu ya gyara zamansa yace “ Allah dai ya sa karshen abin ne ya zo, da har muka sani Allah kuma ya takaita al’amarin”