Page 15
Hajiya Goggo tace "Ameen dai Malam, ni na ma rasa Irin wannan al'amarin, hankalina yayi matukar tashi". "Ki kwantar da hankalinki, babu komai da Ikon Allah, babu wata damuwa mu yi ta addu'a." Ya waiwayi Muhseen yace "Kowane lokaci ka kasance cikin ambaton Allah, kada ka shagala, kuma duk san da ka gabatar da sallarka ta farilla, ka tabbatar ka karanta. Ayutul-kursiyyu kafa uku, Falaki da Nasi kafa uku, su ma. To babu yadda za'ayi wani abin halitta ya cutar da kai . Daga Annabin rahama aka samo wannan garabasar, sal a daure ayi tayi." Muhseen ya rausayar da kai yace "Na gode kwarai, dama ina yi don haka zan cigaba da yi In sha Allah ." Daga nan tattaunawa suka yi tayi, har dare yayi sosal, sannan suka bar dan tsohon Malamin ya runtsa, har daki Hajiya Goggo ta kai Muhseen, sal da ta ga kwanciyarsa kamar yadda ta saba a duk lokacin da ya zo garin. sannan ta rufo masa kofa, ta tafi nata bangaren cikin mutuwar zuciya da tunanin gudan jinin jikanta. Babu wani cikakken barci da Muhseen yayi, illa tunanin daya mamaye zuciyarsa. Kowane dan-adam akwai irin rayuwar da Allah ya tsara masa. Amma tabbas ta shi rayuwar tayi tsauri. Allah ya jarafce shl ta inda bai taba tsammani ba. Shin wace halitta ce ke dawainiya da zuciyarsa? Da wa yake soyayya? Kullum tunani da addu'arsa bai wuce Allah ya bayyanar masa da abin da ke cikin duhu ba, yana matukar son ya san inda rayuwarsa ta dosa, ga kuma maganar Haneefa da ake neman a karfafata. Alhalin baya jin kaunarta ko da kwayar zarra a zuciyarsa, cikin wanan tunanin yake har karfe ukun dare. Wanda daga wannan lokacin barcinsa yake karewa. Domin a al’adar rayuwarsa tun daga lokacin yake tashi yayi brush ya dauro alwalarsa, yayi ta gabatar da sallar nafila har zuwa lokacin da za'a kira sallar asubah. Yau ma haka ce ta kasance a gare shi. Bayan yayi brush ya dauro cikakkyar alwalarsa, ya shiga gabatar da nafilarsa. Bai tashi ba, sal da ya idar da sallar asuba. Sannan ya dan taba barci, wanda ya kai shi har karfe goma dai-dai na safe. Yana tashi yayi wanka ya kintsa kansa, yana cikin daura agogo a tsintsiyar hannunsa Haneefa tayi sallama, cikin sassanyar murya.