KALUBALE BOOK 1

Page 16

by @yargidanimam

Bai dubeta ba, ya amsa har kasa ta duka ta gaida shi. Ya amsa kamar kullum cikin tamkewar fuska da tsare gida cikin taushin murya tace "Babban Yaya Hajiya Goggo tace nan za'a kawo maka kayan karyawarka". A karo na farko ya dago ya dubeta yace "Ki ce mata ban saba karyawa ni kadai a daki ba, tare da ita nake karyawa, Idan kuma yau bata bukatata kusa da ita ne, to a bar batun karyawar, dama ba na jin yunwa." Haneefa tayi dan murmushi, lokaci daya ta tashi tana cewa "Idan aka takaita maganarka ka na nufin ba za ka karya ba, sai a dakin Hajiya, haka zan shaida mata" Ta fita tana murmushi yayi dan matsakaicin tsakl, yace "Saboda kawai na ga Haneefa shi yasa Hajiya ta turo min da wannan sakon, tunda ta san cewa tare muke karyawa, duk san da nake tare da ita." A fill yake maganarsa, daga bisani ya tashi yana cewa "Nan da awa daya ma, ni na bar garin". Daga nan ya fice, kai tsaye falon Sheik Sadisu ya wuce, zaune kan kujera da wani Iittafin larabci ya same shi. Duk da Shelk ya tsufa, amma akwai shi da kokarin karatu, domin kullum Cikin nazari yake, har kasa Muhseen ya zube ya gaida Sheik. Ya amsa clike da so da kauna, ya kara da cewa "Magajin Mallam, amma dai ba yau za ka koma ba? Yayi da murmushi yana kokarin zaunawa a kujerar da take fuskantarsa yace "Na san ba-ka gaji da ganina ba, amma dole yau zan koma, karyawa kawai zan yi, na je gida, na gaida su Hajiyata, sannan zan zo na yi haramar komawa bakin aiki". Sheik Sadisu yace "To Allah ya bada Sa'a, yasa komai ya kasance maka cikin dace yayi maka albarka yasa alheri a cikin rayuwarka" cike da fara’a da kaunar sa Yace "Ameen". Daga nan ya mike ya nufi dakin Hajiya Goggo, ransa a bace, tana zaune da farantin abinci fuska cike da fara'a tace, tana kokarin hada ido da shi "Haba bawan Allah, wannan dacin ran, ina za ka kai shi? Ya zauna yana kallonta yace "Wajenki zan kai shi". Cikin murmushi tace "Mena yi ne?" Ta tambaya, yace "Tsakani da Allah, menene manufar aiken da ki ka yi min? Kin fi kowa sanin cewa tare dake nake karyawa idan kuma kin yayeni ne, ai kamata yayi ki gaya min tun farko." Tayl dariya sosai tace "To sarkin zafi. Shi kenan dan laifin