Page 17
nawa ko? To ayi hakuri, tunda dai matar na tuba, bata rasa mijin aure. Ya lumshe kyawawan idanunsa, ya bude yace 'Shi kenan Hajiya na hakura tunda kinsan bana iya fushi da ke” tayi dariya tace “ To nagode” gaba daya suka sa dariya, lokaci daya tace . "Haneefa". Ta kwala ma Haneefa kira. Da sauri ya dubeta yace "Menene kuma, Hajiya me za tayi miki? Ta dube shi tace "Ina son ta tsiyaya ma kunun ne a kofi, idan kuma ruwan shayin zaka sha, to duk sal ta hada maka". Haushi da Mamakin maganar Hajlya Goggo ya kama Muhseen, ya tsareta da ldo yace 'Da can Ita ce take min duk abinda ki ka Ilssafa? To shi kenan na lura ba kya bukatar na karya." Ya tashi da sauri dai-dai lokacin da Haneefa ta shigo. Ya juya zai fita. "Magajin Mallam ka dawo ka karya, domin ni ma ban karya ba. Kai nake jira." Ba tare daya dawo ba, yace "Ki yi gaggawar karyawa, ni a Kaduna zan karya." Kafin tace komai ya riga ya fice a gaggauce. Duk irin kiran da Hajiya Gwaggo ke masa bai sa ya dawo ba, haka itama Haneefan ta bishi da kallo cike da jin haushi. Gaba daya fuskarta ta canja. Hakan yasa hajiya Gwaggo tayi kamar ba taga halin da ta shiga ba don bata son tattauna maganar. Karfe goma sha daya da minti blyu. Muhseen ya tsaida motarsa a harabar gidan mahaifinsa Alhaji Usman Sadisu Jlgawa. Gida ne me matsakalcin girma, sai dai yana da matukar kyan tsar, ginin zamani ne, komai ya jI. Cikin natsuwa da mutunta kai. Muhseen yayi sallama, Kanwarsa Sakina ce ta fara ganinsa. Da sauri ta'aje robar hannunta, ta nufo shi tana yi masa sannu da zuwa. Ya kamo hannunta ya rike har cikin falon. Hajiya Hadeeza mahaifiyar Muhseen ce, zaune a kan kujera, sauran kannansa su hudu suna zube a kasa a gabanta. Hira suke. Ganin Muhseen yasa duk suka mike suna yi masa sannu da zuwa. Bayan ya zauna, daya bayan daya suka gaishe shi cike da ladabi. Daga nan kowannensu ya fice, ya rage daga Muhseen sai mahaifyarsa, wacce tun shigowarsa idanunta na kasa, babu alamar jin dadin ganinsa a fuskarta. Wanda sam! Hakan bai dame shi ba. Domin ya riga ya saba da hali da dabi’ar mahalfiyarsa a gare shi, bata damu da shi ba, ba shi a cikin tsarin ta,, ba shi a cikin lissafinta, bata san abinda yake so ba, bata san wanda baya so ba, bata san lafiyarsa, ba bata san cutarsa ba. Laifinsa daya, don yana dan fari a gareta, shine ta dauki kunya da kau da kai irin na mutanen da ta dora masa.