KALUBALE BOOK 1

Page 18

by @yargidanimam

Da kam, abin yana damunsa, ya zama tamkar KALUBALE a rayuwarsa, domin bai san kaunar uwa ba. Amma tunda ya mallaki hankalin kansa, ya tursasa ma kansa hakuri da dangana akan batun mahaifiyar tasa, domin ya tabbatar ba za ta canja ba. Har kasa ya durkusa ya gaidata, tunda ta amsa sau daya, bata kara magana ba, tsawon mintina goma. Babu wanda ya kara Magana. Har zaman ya gundiresu gaba daya, a sanyaye Muhseen yace "Dama na zo na yi muku sallama ne, zan koma." A dakile tace "Allah ya klyaye hanya". Daga nan ta juya kanta. Muhseen ya numfasa, yau yana ganin shan mur da nuna Jin haushinsa yayi yawa a fuskar mahaiñyarsa, da gani tana da damuwa da shi, tana da maganar da take son ta gaya masa. Amma bakin cikin Muhseen daya ne, ya san mahaifiyar tasa ba za ta taba iya bude baki ta gaya masa maganar dake ranta ba, sai dai tayi ta nuna masa fushi da bacin ran da bai san dalilinsa ba, yana shirin tambayarta kenan sai Alhaji Usman ya dage labulen falon. Ya shigo yana dubansa ya nemi kujera ya zauna . da sauri. Muhseen ya durkusa kasa yana gaida shi. Shi ma ya amsa, ba yabo, ba fallasa. Kafin daga bisani ya gyara Zamansa yana kallonsa, duk Muhseen sai ya sami kansa da muzanta, duk ya kosa ya tafi, don haka yace 'Dama na zo na dubaku ne, na yi muku sallama, zan koma yanzu." Alhaji Usman ya jinjina kai yace "Ko ba-ka zo ka duba mu ba, lafiya lau muke, ka ji ko? Dama ka tafi, ba-ka zo ka duba mu ba, da ya fi, domin hakan ba zai sa ka faranta mana ba." Muhseen ya nisa cike da damuwa yace "Alhaji Meye faru, me ya kawo irin wannan maganar? Don Allah ka yi hakuri, ku sassauta min haka nan.” Alhaji Usman yace a fusace "An ki a sassauta ma kan, nace an ki. Muhseen ka na neman ka ja min abin kunya da bakin jini cikin Yan-uwana, yanzu meye amfanin maganganun da aka yi tayi a kanka jlya? Meke damunka ne, menene haka? To na gajl, sa maka idon da ake y, shi yasa haka. To ina tabbatar maka da cewa zan yi mummunan saba maka". Ya hadiye yawu, yana ci-gaba da duban rikitacciyar fuskarsa, ya ci-gaba da cewa "Duk a cikin yaranmu kai ne babba