KALUBALE BOOK 1

Page 19

by @yargidanimam

Muhseen ka yi girma akalla yanzu kai me Yi ma wani fada ne arayuwa, ka dubi Kabir da me sunan Mallam (Sadisu), duk Kannenka ne, uwarku daya, ubanku daya, amma ka duba ka gani, daga Kabir har me sunan Mallam 'Ya'yansu uku-uku, amma kai gotai -gotai da kal, ka tsaya kana shirme, ka na shiriritar banza da wofi. To na rantse, wannan babban KALUBALE ne a rayuwarka." Karo na farko Hajiya Hadeeza ta watsa ma Muhseen harara tace "Don Allah Alhaji ku kyale shi, yayi duk abinda ya ga damar yi, rayiwa ce, idan yana ganin burgewa ce yake yi, to ya cl-gaba shi yake tauye rayuwarsa” A kufule take maganar. Rayuwar Muhseen tayi matukar baci, jikinsa sai fitar da zufa yake, wato dai kowa a kufule yake da shi, kowa haushinsa yake ji. Yau gashi har mahaifiyarsa ta fitar da abinda ke ranta. Alhaji Usman ya dawo da kallonsa ga Muhseen yace 'Hajiya Sa'a ta zo gidan nan jiya da daddare, kuma ba komai ba ne ya kawota, sai don ta kara tabbatar mana da abinda ta fada wajen taro. Ta nuna min ba gudu, ba ja da baya, lalle ta ba-ka Haneefa. Hajiya Sa'a "yar-uwa tace, ni na sha nono, na sakar mata, ka fi kowa sanin hakan. Don haka 'yarta, 'yata ce, dole na so-ta kamar yadda zan so 'Ya'yan cikina, kuma tunda ta nuna damuwa akan al'amarinka, ta kuma furta, ta ba-ka Haneefa. Ba ni da wata jayayya akai, don haka tunda ka tsaya ruwan Ido da shiririta da sakarci, to na bada goyon baya, na amince da Haneefa a matsayin matarka. Yanzu ya rage ruwanka, duk abinda ka ga za ka iya, shiza ka yi idan zaka bijire min ne kuma shikenan “ Muhseen ya goge zufar saman goshinsa yace cikin sarkewar murya "Idan na bata muku ne, to ku yi hakuri, ku yi min afuwa, ba ni da jayayya da ku. Amma maganar Haneefa mallam ya ba ni lokacin na yi tunani, kuma kuma Ina rokon alfarmarku, kuma ku ba ni lokacin tunani, don Allah, ba don na lsa ba." Hajiya Hadeeza ta kara sakar masa harara tace "Duk lokacin da ka cinye a baya, bai isheka ba, sai an ba-ka wani lokacin? Alhaji Usman ya daga mata hannu yace "Lokacl ko? “ Alhbuskan ya dube shi rai bace Yace “ Na ba-ka, iya lokacin da Mallam me sangartaka ya ba-ka, ka je ka yi tunanin wanda karshen tunanin ba na sa ran za ka ce a'a, domin a wannan maganar babu a’a” Muhseen ya gyada kai, yace a sanyaye "Na gode".