KALUBALE BOOK 1

Page 20

by @yargidanimam

Daga nan babu wanda ya kara yi masa Magana, daga bisani zaman ya gallabe shi,. Domin jl yayi kamar yana kan kaya, ko yaya ya dubi Hajiya Hadeeza sai ya ga tana sakar masa harara, don haka ya Yunkura ya tashi a darare yace "Na barku lafiya na tafi Allah ya bamu alheri” "Allah kiyaye hanya” Cewar Alhajl Usman, Daga nan da sauri ya fice. Ya sami minti biyu a ciki motarsa, yana kokarin hadiye tashin hankalinsa, gaba daya jigawa tayi masa zafi. Ya kosa ya barta, don haka ya figi motarsa ya koma gidan Shelk Sadisu. Dal-dai karte goma sha blyun rana. Kal tsaye dakin Hajlya Goggo ya wuce. Kwance ya tadda lta, akan doguwar kujera. Haneefa na gefanta, tana danna mata kafafunta. '"'Hajiya zan koma." Ya fada a gajarce cikin bacin ral, ta yunkuro tana kallonsa "Za ka tafi,ba za ka bari ayi azahar ba? “Ya girgiza kai "A'a gara na tafi yanzu, don ban ga abinda zan zauna na yi ba, tunda na gama abinda ya kawoni". Ko bai fada ba, ta san yana cikin bacin rai, wanda bata bukatar ta tambaye shi, domin ta san cewa mahaifansa sune silar. Don kullum ya je gidan da bacin ransu yake dawowa. Ya fito da kudi masu yawa ya aje ma Hajiya Gwaggo a gabanta , nan da nan ta shiga yi masa gidiya gami da sa albarka,Ya juya zai fita, a hankall Haneefa tace 'Da za ka daure, ka taimaki tsohuwar nan, da ka dawo ka karya tukuna, domin har zuwa wannan lokaci bata karya ba, kuma saboda ka ki tsayawa ka karya" Cak! Muhseen ya ja ya tsaya "Mene?" Ya tambaya cike da karin damuwa Haneefa bata kara magana ba, ta maida kanta kasa a hankali. Muhseen ya Juyo ya dawo daf da Hajiya Goggo ya zauna, yana kallonta cike da kauna, yace 'Hajiya me yasa ba ki karya ba? Me yasa ki ka damu da ni? Karte goma sha blyu da minti talatiin fa yanzu, ace har yanzu ba ki sa komai a bakinki ba". Tayi masa kuri da ido tace "Saboda Ina sonka Magajin Mallam, na kasa karyawa, domin na san kaima ba-ka karya ba." Ya ya waiwaya ya dubi Haneefa. Saboda ya faranta ma Hajiya Goggo rai, yasa yace "Haneefa je ki dauko mana abin karyawar". Nan da nan Ta tashi da saurl ta fita. Hajiya Goggo ta dube shi, tayi murmushi tace 'Ashe dai ka damu da ni? “Yayi murmushi yace "Ba dole na damu da ke ba, duk duniya ba ni da masu sona kamar ke da mijinki, ai damuwa dake ya zama farilla Hajiya ta." Ta lumshe ido, tana jin dadin maganarsa har cikin ranta.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam KALUBALE BOOK 1 2009 Tsohuwar Ajiya Daga Habiba Abubakar Imam (Mrs Aliyu Mayere) Bismillahir Rahma Nirrahim