KALUBALE BOOK 1

Page 21

by @yargidanimam

kafin tayi wata Magana, Haneefa ta dawo da kayan karinsu, cikin kankanin lokacl, suka kammala karyawa. Suka yi hamdala. Heneefa na kure musu da ido, "Wannan kauna a jininsu take." Abinda take fada kenan a zuclyarta. Cikin kankanin lokaci, bacin ran Muhseen ya lafa, ya kura ma Hajlya Goggo Ido, yace "Hajiya ku ne kadai masu so-na masu damuwa da lamarina, kuma masu yi min Uzuri “ Ta san Inda maganarsa ta dosa, ta san da mahalfansa yake don tasan kullum cikin rashin jindadin yadda suke nuna masa yake, tace "Magajin Mallam, ba mu ne kadai masoyanka ba, akwai masu sonka da yawa Ciki kuma harda iyayenka, suna sonka kamar yadda ko wane iyaye suke son yayan su." Ya gyada kai yace “ to me yasa ba zasu nuna mun ba ? Allah ya sani bana jindadin irin yadda suke nuna min zai zuciya ta ta fara karaya" Ta girgiza kai tace “ kadaina sa ma ranka wannan damuwar, idan da sabo ai ka riga ka saba babu wani abu sabo a ciki” ya gyada kai yace “Hakane Hajiya “. Ta dan kara kallonsa tace “ Dole dai sai ka tafi yau ba zaka bari sai gobe ba”, ya jinjina kai , shi kansa yana son ya zauna tunda gaba daya bashi zai jagoranci tukin jirgi ba wannan satin, yasan zai iya zama a jigawa to amma wannan maganar da suka bijiro masa da ita ta Haneefa da kuma zuwan Haneefar gidan yasa yake son ya tafi. Don haka dole ya lallaba Hajiya ta barshi ya tafi ba tare da ta hana shi komawa ba yau kamar yadda ya tsara. Saboda hska ya dubeta yace “ Dole na koma yau sabida ina da aiki sosai gobe litinin”. Ta numfasa tace “ Idan hakane kuwa bai kamata na tsaida kai ba, saboda haka kayi sauri ka kama hanya saboda tafiyar akwai nisa”. Da sauri ya yunkura ya tashi, Haj Gwaggo ta dan nuna masa Haneefa da ido, ta kuma sa masa ido, wanda nan da nan ya fahimci inda ta dosa, yana bukatar ya faranta mata rai , don haka yayi mata yadda take bukata. Ya zaro Naira dubu goma ya mika ma Haneefa yace “ Gashi ko kina da wata bukatar”

Ta amsa cike da ladabi tana murmushi tace "Babban Yaya , na gode. Allah ya saka da alheri." Ya yunkura ya tashi yana kallon Hajlya Goggo da take cike da fara'a. "Hajlya zan tafi, sai mun yi waya". Ta tashi ita ma "To Magajin Mallam. Allah ya tsare hanya Allah ya kaika lafiya” ya amsa “ Amin “ Tare suka fito har da Haneefa. Falon Sheik Sadisu ya shiga. Shi ma yayi masa sallama, ya kuma aje masa Naira dubu hamsin. Yasa masa albarka kamar kullum, yayi masa kuma fatan alheri. Haka zallka ya Jaddada masa zama cikin addu'a kallum. Daga karshe Muhseen ya shiga motarsa Honda hala, me sheki da daukar idanu, ta sha kwalliya wacce ta kara mata kyau. Cikin kankanin lokaci ya ja motar, kamar walkiya ya bace akan titl. Zuciyar sa cike taf! Da tunanin wannan kalubalen daya shigo rayuwarsa. Hakika zuwansa jigawa, babu abinda ya halfar masa, face bakin ciki da tashin hankali da kuma ya san haka za ta kasance masa, hakika da bai zo ba.