KALUBALE BOOK 1

Page 22

by @yargidanimam

Karfe biyar da kwata na yamma dai-dai. Haneefa tayi sallama a cikin gidansu, Hajlya Sa'a na yankan danyar kubewa, na miyar dare da tuni ta dora ,tayi saurin dagowa tana kallonta cike da Mamaki, ta kira sunanta "Haneefa." Fuskarta washe ta amsa, lokaci daya tana karasowa kusa da ita "Yana ganki a gida yanzu, me yasa ki ka dawo? Ta zauna kusa da ita cike. Da shagwaba tace "To Hajiya wanda na je dominsa, ya tafi . Ni kuma Zaman me zan yi a gidan ko don dai ayi ta sani aiki, haka kawai". Haj sa’a Ta aje robar da take yankan Kubewar a ciki tace "Me kike nufi ? Kina nufin ki ce min Muhseen har ya bar garin “ Haneefa ta yarfar da hannu gefe tace “ ya wuce, don tun karfe daya ya tafi “ Hajlya Sa'a ta saki tsaki a kufule tace 'Duk taro, idam ya zo kwana uku yake yi idan kuma ya baro aiki kwana biyu yake yi, shine wannan karon ya yi kwana daya rak ya tafi” Ta dakata fuskarta cike da fushi ta cigaba da cewa. “Na san dalllin tafiyar tasa, sabada anyi masa Maganar aurensa da ke ne To karyarsa ta sita karya, tunda na riga na kallafa rai akan aurenku na kuma dorama kaina Sai hakan ya tabbata to .Dolensa ya yi yadda nake so ko yaki ko ya so." Haneeta ta yamutsa fuska tace "Kai Babban Yaya da Jan aji yake da miskilanci. Hajiya ko kin san tunda na je gidan nan, daga ni har Hajiya kokarin masa kaina muke. Ammo har ya tafi na rantse banyi tsammanin ya kalleni sau uku ha, balle fa wata magana ta hadani da shi,sai shan kamshi yake yana hade rai kamar na zo masa da mugun abu” Hajiya Sa'a tasa mata ido cike da takaici tace 'Muhseen ai ya na da wuyar sha’ani, to Ina maganar ladabi da salon jan hankalin da nace ki dinga yi masa? Tayi dan murmushi tace "Na lura Babban Yaya ba irin mazan da mace- ke saurin janyo ra'ayinsu bane, domin duk na yi masa, amma fa bai ma san ina yi ba Hajlya ko kallona ba yayi baima san da zamana ba” shuru Haj sa’a tayi tana kallon Haneefa gami da sauraronta, sannan ta cigaba da cewa "Dama kinfi kowa sanin tun farko ina son yaya Muhseen, amma ban taba sa ma kaina son aurensa ba , sai yanzu da Kika gaya min zaki hada ni aure da shi , sal na sami kaina da kara matukar kaunarsa da kuma son na kasance matarsa, sai ina jin Hajiya tamkar ba zan iya rayuwa babu shi ba . Ina sonsa sosai ." Hajiya Sala tayi dan murmushi

Tace "Haneefa masu gari, kada ki damu kan ki kan muhseen domin bai isa yace bazai aureki ba duk tsiyarsa, domin tuni nake miki sha’ awar aurensa domin zan jefi tsuntsu biyu da dutse daya ne, kin ga muhseen tun yana karami, yaro ne me nasibin rayuwa , zuwa yanzu kuma kinsan dai babu abinda bai mallaka ba yana babban aiki yana da kudi dai dai kasar da bai je ba a dalilin aikinsa na tukin jirgi. Nasan za kiji dadi