Page 23
matukar ki ka aure shi, ni ma kuma zan jl dadi, don haka auren ki da Muhseen kusan nace ya zama dole da ikon Allah." Haneefa ta cika da fara'a. Tana shirin yin magana kenan Dai-dai lokacin Mallam Jibrin ya fito daga dakinsa, ya dogare yana kallon 'ya da uwarta, lokaci kadan ya saki tsakl yace "Hajiya sa'a, don Allah duk abinda za ki yi a rayuwarki ki dinga yi domin Allah". Ta walkato da Idanunta tace "To me kake nufi Mallam? Don Allah kada ka lika min wata Magana, don na sanka sarai yanzu ka fara min wa’azi kamar ni bansan Allah ba." Mallam Jibrin ya girgiza Kai yace "Ba haka bane, na ga ki na kokarin hada Muhseen da Haneefa aure. Akan wani ra'ayi Irin naki, don kawai yana da kudi, . me zal sa ba za ki yi kokarin hadasu domin Allah ba? Ta dan fusata tace "Ka ji matsalarka, don Allah kada ka Kaini gaba, kada ka sanyani a bakin duniya. Muhseen dai da-na ne. Haneefa ma Yata ce, don haka don Allah kada ka shiga maganar nan." Cike da bacin ran yadda a kullum Haj sa’a bata mutunta shi yace "Ba zan shiga ba, tunda ni ba Ya'yana bane, ban haifi ko daya a cikinsu ba, ba ni kuma da iko a kansu". "Ka haifi Haneefà mana, Iko kuwa gaba daya muna da Iko a kanta, amma don Allah ka daure ka rabu da ni, ka sa min Ido" "Na sa miki Idon, amma kada ki manta, shi kansa Idon guba ne" Yana gama fadin haka, ya juya ya fice cikin bacin rai, Sau tari yana mamaki ace wai Hallya Sa'a yar shahararran Malami Irin Shelk Sadisu ce , wanda ba Jihar Jigawa ba, hatta duniya ta san waye shi, ta kuma san iliminsa, amma abinda 'yarsa Hajlya Sa'a take a gidan auranta, ko kare ba zai ci ba. Miji da kowace mace me hankall ke dauka da daraja da mutunci, ita sam! Ba haka bane. Mallam Jibrin bai Isa yace ayi, ayi ba, a matsayinsa na mijinta, sai abinda ta ga damar yi. Kuskure kadan, za ta sa shi a gaba da masifa da fada, tamkar dan da ta halfa. Sau tarl idan tana yin wani abin, sai mutum ya rantse da Allah Hajiya Sa'a bata san komai ba a addini nan kuwa saukakklya ce ta Kur'ani, tun kafin tayi aure ta sauke kur’ani da sauran littafan addini . Jarabarta yasa Mallam Jibirin ya gaji ya kara aure. Amma don dole saboda tsananin bala'in Haj Sa'a, amaryar bata wuce wata uku ba, ta bar gidan da roko da maglyar ya saketa, ba za ta iya zaman kishi da Haj Sa'a ba. Dole ya rabu