Page 24
da Ita, ba don baya sonta ba, sai don kwazabar Hajiya Sa'a, tun daga wannan lokacin kuma, bai kara marmarin kara aure ba, ya ci-gaba da zama da Hajiya Sa'a a matsayin KALUBALE a rayuwarsa. Domin sau tari danginsa gani suke Hajlya Sa'a ta shanye dan-uwansu a matsayinta na 'yar Mallam. shi yasa Mallam Jibrin ke tsoro da shakkarta. Amma gasklyar Magana, babu batun shanyewa, domin tunda Shelk Sadisu yake bai taba ba 'Ya'yansa koda addu'ar da za su mallaki mijl ba, ya riga ya haramta ma kansa hakan Ta bangaren Mallam Jibrin kuma ba wai tsoro da shakkar Hajiya Sa'a yake ba, a'a yana gudun duk wani abu da zai lya taba masa mutuncinsa ne, domin ya san bata da kunyar ci masa mutunci a gaban kowa. Shi yasa yake kokarin mutunta kansa, sai kuma arziki da albarkar Ya'yan dake tsakaninsu har guda shida, wanda dukkansu sun mallaki hankalin kansu, shi yasa baya kaunar su dinga raba abin fada a gabansu. Hajiya Sa'a ta dubi Haneefa tace "Autar mata, kin ga halin mahaifinku ko? Duk san da alheri zai iso garemu, kokari yake yayi mana katangar karfe da alherin, na rasa dalilin hakan. Domin dai ko ban fada ba, auranki da Muhseen alheri ne.” Haneefa ta fadada fara'arta tace "Kuma zai zama abin alfahari gareni, don na sani ba ni kadai ce ke sonsa a cikin 'Ya'yan 'yan-uwana ba, don haka kin ga idan na same shi. Ai na daga tuta." Hajiya Sa'a tace "Autar mata, zan Jajirce tare da dagewa, domin na tabbatar da auranki da Muhseen, kada ki damu, ke dai a koyaushe a gabansa ki dinga kokarin nuna masa hali na-gari kamar yadda na tsara miki. Kada ki nuna masa halinki na shirme da ki ka saba, kin ji? Haneefa ta gyada kai lokaci daya ta tashi tana dauko kudin da muhseen ya bata daga cikin Jakarta ta mika ma mahaifiyarta, tana dan murmurshi "Ga shi Hajiya, Babban Yaya ya ba ni kyauta. Naira dubu goma ne" Hajiya Sa'a ta amsa cike da fara'a tace 'lye, lalle har na jidadi domin wannan ya tabbatar min da cewa Muhseen yana da ra'ayi a kanki, illa miskilancinsa da yake hana shi sakewa."