Page 25
Haneefa murmushi kawai tayi,ta juya ta shige daki. Hajlya Sa'a ta sa ma kudin ido, tana dan murnushi. Zahiri a yanzu bata da wan buri daya wuce auran Muhseen da Haneefa, sai kuma Inda Karfinta ya kare, ba za ta yi lakwa-lakwa ba, domin ta san ba ita kadal ke kwadayin hada 'yarta da Muhseen ba, kaf! Yan-uwanta, ta san babu wanda baya so da kaunar ba Muhseen "yarsa, don haka ba za ta saurara ba. Muhseen Usman jigawa ne Kishingide akan tattausar kujerar falonsa, yana lumshe da kyawawan Idanunsa, jikinsa na sanye da riga da wando masu taushi.Karfe bakwai ne da kwata na yamma. Amma kasancewar ba'a dade da dauke ruwan sama ba, ya sa garin yayi dan duhu tamkar dare yayi sosai. Gefensa kan ( daining table), cike yake da kayan abincl, wanda kukunsa ya kammala hadawa. Tsawon awa daya da ta wuce. Muhseen cikin zurfin tunani yake, tsawon mako daya kenan da dawowarsa daga Jigawa. Amma har zuwa wannan daren, abinda ya faru a jigawan bai bace masa ba. Kullum cikin matsanancin tunani yake da kokarin samo ma kansa mafita. Amma ya rasa. Yadda zai bulloma lamarin, usman ya yi sallama cikin falon, usman shine abokin Muhseen sosai bayan kasancewarsa abokin aikinsa akwai karfin amintaka a tsakaninsu. Kai tsaye inda teburin cin abinci yake ya nufa yana cewa "Abokina ko ka yi ragowar abinci a gidan nan? Yunwa nake ji”. Muhseen yace ba tare daya bude idonsa ba "Karasa (Daining table), akwai abincl." Umar ya wuce a hanzarce ba tare daya damu da ganin halin da Muhseen ke ciki ba, haka zalika bai waiwaye shi ba, har sal da ya gama cika cikinsa da abinci, sannan ya taso ya zo kujerar dake kusa da Muhseen ya zauna, yana kokarin kallon fuskarsa. "M.U Jigawa." Ya kira sunansa, kamar yadda suka saba kiransa, ya amsa ba tare daya bude idonsa ba. Umar ya dan numfasa yace "Ba zan gaji da tambayarka abinda ke taba rayuwarka ba, domin a tunani na damuwarka tana da nasaba da damuwata, don haka nake tunanin dalilin da yasa ba za ka iya sanar da ni abinda ke damunka ba, tun bayan dawowarka daga Jigawa, gaba daya duk ka canja kullum kana cikin tashin hankali da damuwa, ga rama ka fara yi , kullum ina tambayarka abinda ke damunka amma ka ji gaya min, amma udan kana ganin tamkar ban cancanta nasan damuwarka ba ne shikenan “, ya karasa magana fuskarsa na bayyanar da fushi.