KALUBALE BOOK 1

Page 26

by @yargidanimam

Muhseen ya bade idanunsa gaba daya masu cike da damuwa, ya dora akan fuskar Umar, sannan ya numfasa yace "Umar na ki gaya maka damuwata ne. Saboda Ina tunanin zan iya shawo kan matsalata da kalna, ba tare dana nemi shawarar kowa ba, amma na fahlmci al'amarin ya gagari tunanina. Umar ina cikin damuwa." Umar ya nisa yace "Na dade da sanin hakan, yanzu abu daya ya rage, shine na san damuwar, domin mu san hanyar warwareta." Muhseen ya sauko da kafafunsa kasa ya hada hannayensa biyu ya zuba su akan fuskarsa yana kallon Umar yace *Aurel Umar maganar aure ke damuna. Zuwana jigawa na fahimci yadda dangina gaba daya ke Jin zafin rashin yin aurena har zuwa wannan lokacin, kowa cikin zafl yake da ni. Kowa gaya min magana yake me matukar zaf. Umar suna ganin rashin aurena tamkar ra'ayina ne, haka kuma nake so". Umar yace yana kallonsa "M.U jigawa , kai ma ka san dole ka sami Irin wannan matsalar, domin maganar gaskiya, aure shine kadai ya rage ka cika darajarka, batun ace ka isa aure ma, ina ganin tsohuwar magana ce, domin ka isa aure. Har ka wuce, ka dubeni, ka girmeni, amma Ya'yana hudu. Ni ma a matsayin ban yi auran akan lokaci ba, dole su damu kasancewar jama'a da dama za su dinga yima kallon kana shashanci da neman mata a waje, domin za su ga kamarka, karya ne ace ka kawo warhaka ba-ka da aure. Kuma ka ya danne sha'awarka akan *ya mace.”. Muhseen yakamata ka sami natsuwa, ka na da illmi yadda mu kanmu muna alfahari da illminka, to me zal sa ka zauna shaldan na wasa da Imaninka?”. Muhseen ya runtse idonsa ya bude yace "Umar ba na jin wanl abu a game da wata 'ya mace, ba na jin sha'awa ko soyayyarta, wanda ka san dalill, ba ni da bukatar kara sanar da kal". Umar ya dafa kafadarsa yace "Wannan shaidan ne Muhseen. Shaidan ne kawai ke wasa da hankalinka, wannan halittar Idanun dake hanaka sakat a cikin barcinka da lokacin da kake farke,