KALUBALE BOOK 1

Page 27

by @yargidanimam

ba kowa bane, face shaidan. Yakamata kuma ka yi maganinsa kada ka bari ya ci galaba a kanka abokina." Muhseen ya dube shi yace 'Ka na ganin haka ne?" Ya gyada kai yace "Kwarai da gaske kuwa". Muhseen ya saki ajlyar zuclya yace "Umar ba ni shawara, kokarl ake a hadani aure da 'yar kanwar mahalfina Haneefa, kowa ya amsa. Ni kadai ake jira, yaya zan yi Umar? Amma fa ba na son yarinyar. Ban yi zaton kuma zan iya sonta ba, to meye abin yi?” Umar yayi shiru alamar tumani sannan yace "Batun ka ce za ka bijire musu ma, bai taso ba, tunda ba ka da wata wacce za ka kal musu, ka ce za ka aura, balle su fasa maganar, saboda haka a ganina ka yi hakuri kawai , ka amince da zabin nasu, wanda na san za su ji dadi, za ka wanke musu bacin ran da ka sa su a ciki. Shi kuma so ai a hankali yake samun matsuguni a zuciyar mutum. Don haka na tabbatar matukar ka manta da shashashan mafarki da wadannan firgitattun idanun, to za ka so yarinyar, za kuma ka ji dadin zama da ita, tunda biyayya ka yi mutumina", Muhseen yayi shiru kamar ruwa ya cl shl. Shi kansa zai so ya bi shawarar Umar, ko don ya faranta ran kakaninsa da mahaifansa, amma yana jin tamkar ba zai lya ba, domin ma sai ya sami kansa da tsanar Haneefa fiye da duk Irin tsanar da yayi ma wata 'ya mace. Shi yasa yake jin tamkar ba zai lya bin umarninsu ba, akan auran Haneefa. Zuciyarsa a cushe take, kullum, a dalilin maganar auransa da Haneefa. Umar yace a hankali "Ka daure, ka cije, ka yaki shaidan ka ba mara da kunya, ka tabbatar ma da magabatanka amincewarka akan zabinsu, domin hakan ma samun wata daraja ne." Muhseen ya rausayar da kai yace "Na gode Umar, ni ma kuma zan yi nazari akan shawarwarinka, na gode." Umar ya mike yana kallonsa "To shi kenan, Allah ya zaba abinda ya fl zama alheri, ni zan tafi , sai da safe." Ya daga masa hannu a hankali yace "To sai da safe Umar." Daga nan Umar ya fice ya bar Muhseen cikin dogon tunanI da lissafi.