KALUBALE BOOK 1

Page 28

by @yargidanimam

Tun makon daya gabata, aka fara shirye-shiryen bikin Ya'yan Alhaji Sani wanda ke bi ma Hajlya Sa'a. Na yarsa daya Nafeesa, da dansa namijI Hassan. Rana daya ne bikin, za'a fitar, za kuma a shigar, don haka gagarumin sha' ani za'ayi a cikin zuri'ar Sheik Sadisu, kodayake dama tunda ake aure-aure, ba'a taba aurar da mutum daya ba, domin dai Alhamdulillahi. Zurl'ar Sheik Sadisu tana da yawa kwarai da gaske. Shirye- shiryen biki ya kankama. Amarya an gama komai na dakinta, shi ma kuma Hassan din an kammala komai na batun kayan lefe, domin a yau asabar ne su Haliya Sa'a suka kai kayan lefen,, wanda komai ya yi babu abinda ake nema a ciki wanda ba’a sa ba . Ta bangaren Muhseen kuwa, duk da yana kaunar halartar bikin, gaba daya sal ya sami kansa da rashin son zuwa jigawa, domin yana gudun duk wani abu da zai sa ayi masa maganar aure, wanda ya san dole ne ayi masa maganar, kasancewar Hassan kanin-kanin bayansa ne. Ya girme shi nesa ba kusa ba. Auransa zai kara ja masa abin magana da surutu a cikin dangl. Amma ya zai yi? Babu yadda ya lya, dole ne ya je bikin, domin ya zama dole a gare shi. Sal dai ya toshe kunnansa, saboda bikin su Hassan yasa aka daga taron dangin da suke yi , domin ya kama rana daya da ranar daurin auren. Tun ranar Juma'a Muhseen ya shirinsa na zuwa jugawa . Haka zalika ya jl dadin yadda Umar yace zai yi masa rakiya, domin shi ma yana kwadayin halartar bikin, don haka karfe blyun rana Muhseen da Umar suka bar Kaduna. Suka nufo jigawa . Muhseen yana cikin wani yanayl na damuwa, wanda yake kokarin boyewa. Da isarsu jigawa . Tun daga kofar get din gidan Sheik Sadisu. Umar ya fara fahimtar muhimmancin Muhseen a gidan, suna shiga cikin gidan , ihu da murnar Jama'ar gidan kadai ya isa ya tabbatar ma da Umar matsayin Muhseen. Cikin sauri da gaggawa Hajlya Goggo ta fito cike da fara'a 'Magajin Mallam, kirana ne ya sameka? Domin duk sallar da zan yi, sai na roki Allah yasa ka taho yau, ba sai gobe ba."