Page 29
Yayi murmushi yana kallonta yace "Ni ma duk na kosa nã zo na ga kyakkyawar matata, don haka ko ba kiranye, zan zo Hajiyata." Gaba daya suka sa dariya. Yayin da ta dubi Umar tace "Tare kake da bako ne? Ku shigo mana." Muhseen ya wuce tare da Umar zuwa falon Hajiya Goggo, yana bata amsa "Abokina ne Umar, yayo min rakiya." Dukkansu kujera suka zauna, tana kallon Umar cike da fara'a tace 'Ka ce me babban suna ne. Babana ne, na kaina. Lalle ka kyauta da ka ziyarcemu a dai -dai lokacin daya dace. Ya hanya? Umar ya zamo daga kan kujera ya gaidata , shi ma Muhseen har kasa ya zube ya kwashi gaisuwa , cike da so da kauna da fara'a, ta amsa masa. Daga gani, tana cikin jin dadi da annashuwar ganinsa, kan ka ce meye wannan? Tuni har an fara cika gabansu Muhseen da kayan abinci, sun ci abinda zasu iya ci . Daga bisani suka bar dakin Hajiya Goggo zuma falon Shelk Sadisu. Gidan ya fara cika da jama'a, domin duk cikin Ya'yan Sheik Sadisu. AlhajI sani ne kawai bal fita daga gidan gado ba, shi da matansa guda blyu. Haliya Binta da Hajiya Shafa da 'Ya'yansu. don haka dole gidan Shelk ya clika, tunda kowa ya taho bikin nan zai yada zangonsa . Shelk Sadisu yana zaune akan kafet ya jingina jikin filo da alamar son hutawa a tare da shi. Amma yana ganin Muhseen, ya yunkura ya tashi cike da fara'a, yana kiran sunansa. Kusa da jlkinsa sosai Muhseen ya zauna, yayin da Umar ya sami gefe daya, ya zauna, yana kallonsu cike da sha' awa. "Malam kana lafiya? "Lafiya lau nake, Magajina, Ina Kwancen nan, maganarka kawai nake a ciki zuclyata. Ashe ka na kusa da ni. Ya hanya? Ya amsa "Lafiya kalau, Malam, ya shirye- shiryen biki?”, Ya dan karkace kai yace "Masu yi na, nan na yi, ai ni bikinka ne za'ace min ya shlye-shirye, ina kuma addu'ar Allah yasa ayi, ina raye'. Cikin murmushi umar yace "Ameen". Nan da nan ya dubi Umar a yayin da Umar din ke kokarin gaida shi , ya amsa ya kara da cewa “ kayi hakuri matsalata kenan idan naga magajin mallam ido na rufewa yake yi bana ganin kowa, Tare kuke Magajin Malam? Muhseen yayi murmushi yace "Tare muke. Malam, abokina ne sosal, domin duk cikin abokan aikina bani da wanda ya fishi, tare muke yun komai “.
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan imam KALUBALE BOOK 1 2009 Tsohuwar Ajiya Daga Habiba Abubakar Imam (Mrs Aliyu Mayere) Bismillahir Rahma Nirrahim