Page 30
kusan tare muke komai. Dan Katsína ne shima" Sheik ya dubi Umar sosai yace "Na ga alamar kamala a tare da shi, dama na san ba-ka abokin banza, to ya batun aure, ko kai ma kana layin abokin naka? Tunda ance zama da madaukin kanwa , shi ke kawo farin kai." Umar yayi murmushi yace "Mallam Ina da mata da 'ya'ya hudu". Ya jinjina kai yace "Da kyau Umar, Allah ya kawo ranar da shi ma abokinka za'ayi masa tambaya, irin wannan ya bada amsa irin taka." Umar yace cikin dan murmushi "Shi komai lokaci ne Mallam, sai dai a kara hakuri", Ya numfasa yace "Haka ne Umar. Allah yayi mana da kyau". Muhseen ya dube shi yace 'Don Allah a bar maganar haka, Mallam daga zuwana ko hutawa ban yi ba, ba na son a dinga yi min Irin wannan maganar." Shelk yace "Tuba nake. Allah ya huci zuciyar Magajin Mallam," gaba daya suka sa dariya. Sun ci-gaba da zama cikin hira me dadi da wasa da dariya. Wanda Umar ke JIn matukar dadin hirar, domin duk abinda zai fito daga bakin Sheik na karuwa ne da darasi. Kiran sallar magariba ya tilasta musu tsinke duk wata hira. Suka tashi domin gabatar da farali. Sheik Sadisu ne ya jasu limanci, a masallacin dake harabar gidansa, kamar kullum masallacin cike yake da jama'ar gida dana waje, bayan idarwarsu, wa'azi da fadakarwa Sheik Sadisu yayi tayl a cikin masallacin. Babu wanda ya matsa har zuwa lokacin da aka kira sallar isha' I. Nan ma ya tashi ya jasu sallar, bayan idarwarsu, Jama'a duk suka watse. Ya rage daga Sheik Sadisu, sai Muhseen da Umar, don haka ya ci-gaba da yi musu wa'azi. Kwarai da gaske Umar yana jin dadin wa'azin, domin yana matukar karuwa da abubuwa da dama, wanda da bai sani ba. Sai karfe tara suka fito daga masallacin. Sai da suka ga shigar Sheik falonsa, sannan Muhseen da Umar suka nufi bangaran Alhaji Sani, bangaran nasa cike yake da mata, kusan duk 'Ya'yan Yan-uwansu mata, marasa aure suna dakin Hajiya Binta mahaifiyar amarya Nafeesa. Ciki kuwa har da Haneefa, sai hayaniya da surutai tamkar za su tashi dakin sama. Amma sallamar Babban Yaya ya haddasa ma kowa natsuwa a falon. Kowacce a hankali take yi masa sannu da zuwa, duk suka sauka daga kan kujerun, wanda hakan ya ba su Muhseen damar zaunawa akan kujerar. Daga nan kowacce ta gaishesu, suna satar