KALUBALE BOOK 1

Page 31

by @yargidanimam

kallon Muhseen. Amma Haneefa idonta kirr! A kansa, burinta daya su hada ido da ita, ya san tana cikin falon. Amma gogan naku, babu wacce ya daga kai ya kalla, amma Umar gaba daya sa musu ido yayi, yana matukar yaba kyawun da Allah ya ba su. Daga gani, babu tambaya duk 'Yan-uwan juna ne, domin suna kama da junansu. Cikin dabara ya kirgasu, su goma ne cif! Kowacce ta cika mace, ta kai munzali, miji kawai suke jira. Dai-dai lokacin Hajlya Binta ta shigo cike da fara'a ta dubi su Muhseen tace 'A'a mutanen Kaduna ne? Har an Iso. Amma dai ba yanzu kuka shigo ba, don na san ba-ka son tafiyar dare." Yayi dan murmushi yace "Mun dade da zuwa, Ina gajiya? Daga nan suka gaisa, ya gabatar mata da Umar suka kara sabuwar gaisuwa. Muhseen ya dubeta yace "Baba ya fita kenan? “ Ta dan gyara zamanta tace "Eh! Ya fita, amma bai Jima da fita ba". "Hassan fa? Muhseen ya tambaya, tace "Ai Hassan ba zama, ya shigo, ya fita.." "Muhseen yace "Ai dole ne, ba zai huta ba, har sai ya mallaki 'yar amaryarsa." Tayi dariya tace 'Ai fa kam, saura kai, kaima Allah dai ya nuna mana naka haka, Allah yasa muna raye”. Umar ne yayi saurin amsawa da “ Amin”. Nan da nan Muhseen ya yunkura ya tashi, domin baya son ta ja maganar da nisa a gaban Kannensa da suka sa masa ido, tamkar za su ga bayansa, kowacce ta kafe idona a kansa "Bari mu je mu gaisa da Hajiya Shafa." Ta giriaza kai "Tare suka fita da Alhaji sai dai idan sun dawo, saika dawo ku gaisa” muhseen yace,

'"To shi kenan. Umar mu je". Umar ya mike suka fice. Suna fita, gaba daya 'yan matan dakin suka sa shewa, suna kallon Haneefa. Haliya Binta ta dubesu tace "Menene haka? Ku dai ba kwa gajiya da shiririta." Tana gama fadin haka, ta juya ta fita. Daga nan ne Haneefa ta dubesu tace "Meye, don wulakanci sai kun dubeni, sannan ku yi shewa? Ni ba ni son wulakanci." Nana ta dakatar da Ita tace 'Ba dole mu yi shewa ba, dazun nan ki ka gama fasa kai akan Babban Yaya, ki na gaya mana ya mutu miki, yana sonki zai aureki, sai ga shi ya zo, kamar ma bai taba ganinki ba." Zulai tayi dariya tace 'Dama kin daina rawar kai akan wannan mutumin, domin kowaccan mu tayi, ta bari, babu wacce bata son auran shi a cikinmu, amma ya zamu yi? Tunda bai san muna yi ba, kuma ba shi da lokacinmu. Shi yasa na yi mamaki da kika ce yana sonki ya kuma yarda zai aure ki, domin ni tunda nake a duniya ban taba ganin miskilin mutum irin yaya Muhseen ba ga rashin sakin fuska”.