KALUBALE BOOK 1

Page 32

by @yargidanimam

Ta dan numfasa sannan ta cigaba da cewa “ shi yasa tuntuni nayi ma kaina karatun ta natsu na cirema kaina sonsa na rungumi me sona Ayuba, kema gara ki hakura ki nemi wani shawarace nake baki”. Ran Haneefa yayi matukar baci cikin fusata tace "Duk na fahimceku, hassada da bakin ciki ke damunku, saboda ni na samu yana sona, to sai dai ku mutu domin aurena da yaya muhseen babu fashi sai dai bakinciki ya kashe ku." Bilki ta saki tsaki tace "Bakin cikin me? Babban Yaya dai ga ki nan, ga shi, mu meye namu? Baiwar Allah." Gaba daya suka kara kwashewa da dariya, a fusace Haneefa ta tashi ta dau gyalenta "Sai da safenku." Nana tace "Kin fasa kwana anan din? Ta sakar musu harara tace "Idan amaryar ta shigo, ku gaya mata kun koreni." Daga nan bata jira komai ba, ta fice cike da fushi, da jin zafin maganganum 'Yan-uwanta. Gaskiya Muhseen ya bada ita. Tana shiga falon Hajlya Goggo, ta dubeta a turbune tace "Hajiya zan tafi gida." Ta dago tana kallonta tace "Gida kuma haneefa? Ba nan za ki yi Kwanciyarki ba? Tayi shiru ta ci-gaba da cewa 'Kin san Magajin Malam dazun nan ya shigo?”,Haneefa ta lalubi kujera ta zauna, tace 'Na gan shi mana Hajiya. Shi yasa ma zan tafi gida". 'Me yayi miki?" Ta tambaya a gajarce. Haneefa tace 'Cikinsu Bilkisu ya nuna kamar bai taba ganina ba. Alhalin na riga na gama cika musu bakin cewar yana sona ko zai wulakantani ai bai kamata ya wulakanta ni a gabansu ba”. Hajlya Goggo tayi murmushi tace 'Kai Haneefa da rigima ki ke, me yuwuwa ma bai ganki bane, kuma bayan haka ma, ba kin san halin babban yayan naku bane, na kauda kai. Ai yakamata ace kin San hakan, kuma sanin kanki ne har yanzu Magajin Mallam bai furta ya amince dake ba, ni Ina ganin ai sai a hankali ko? Kuma fushin fari, ai ba naki bane, ba dai ke ki na sonsa ba?” Ta daga kai alamar "Eh." Tace "To tunda ki na sonsa, ki yi ta hakuri, ki daure ki lya da halinsa. Wata rana dole ke ma sai ya so-kl, sai ya rama ma kura aniyarta, kin jI? Amma a yanzu mu za ki taimaka Idan ki ka dage ki ka shanye komai, daga gare shi, domin auranku shine kadai burina a yanzu, saboda Allah ya sani na gaji da ganinsa a haka “, ta karasa magana fuskarta na fitar da sakon damuwa. Haneefa ta numfasa, duk maganar Hajiya Goggo gaskiya ne, tunda tana son Muhseen. Ya zama dole ta daure ta shanye duk irin abinda zai mata komai zafinsa , zata jira har zuwa lokacin da makaman yakin zasu dawo hannunta, daganan itama sai tayi yadda ta ga dama.