Page 33
Domin dai Daga randa ta zama matarsa, komai zai zama tarihi. Hajiya Goggo tace "Maganar tafiyarki gida yanzu babu, dare yayi, kuma kin san halin Sa'a da zafi, dan wannan abun sai ta dauke shi ta aje shi a zuciyarta," "Haneefa ta zame gyalenta ta'aje gami da kwantawa akan kujera tace 'Na fasa tafiya nan zan kwana Haj “, tayi murmushi tace "Yauwa Haneefa, haka nake ,so ki yi kwanciyarki tare da ni". Can dakin Muhseen ko Umar na saman doguwar kujera a kwance Muhseen na kishingide a saman kafet, ba su dade da kammala cin abinci ba. Talabijin na yi, suna kallon wata tasha ta Gamzaki, wacce ake gabatar da fina-finan hausa, suna kallon shirin mu sha kida, wake-wake da raye-raye, sai dai fa daga Muhseen din har Umar, babu wanda hankalinsa. Ke kan Talabijin din kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa. Daidai lokacin da agogon falon, ya buga karfe goma sha daya na dare. Umar ya kauda shirunsu da cewa " Wai M.U jigawa ya kuke da 'yan matan da muka tada a bangaren Baba Sani ne?” Muhseen yadan muskuta yace "Duk kannena ne, domin 'Ya'yan Kannen mahafina ne mahaifina kuma duk shine babba a gidan nan kamar yadda nake babban jika a gidan." Umar ya rausayar da kai gefe yace "A cikinsu ne aka zaba maka wacce za ka aura." Ya gyada kai "A cikin su ne, sai dai ba zan lya siffanta maka kayan dake jlkinta ba, balle ka ganeta, domin sau daya na dubeta, shi ma din banda tabbacin fuskarta na gani." Umar yace "Mutumina, gaskiya kannanka suna da kyau, sai yanzu kuma nake kara tabbatar maka da cewa ka amince da zabin nan, don Allah kada ka yi ma kanka." Muhseen yayi shiru, yana rufe da idonsa. Umar ya ci-gaba da cewa "A dan lokacin dana samu a gidan nan, na fahimci yadda ake kaunarka, kana da matukar muhimmancin a rayuwar gidan nan. Kakanninka na matukar kaunarka, kuma wani abu da ya ba ni mamaki, shine irin matsananciyar kamar da kake yi da Mallam. Kuma duk halayanku daya ne, na son addini. Mallam ya tsufa Kwarai, amma yana da karfinsa da son yin karatu, don Allah menene sirrin kaunar da suke maka Muhseen?.” Ya dan gyara kishingidarsa ya juya yana duban Umar, sannan yace "Saboda tare da su na taso, tare na yi rayuwata da su,