KALUBALE BOOK 1

Page 34

by @yargidanimam

domin tun Ina dan shekara uku na bar hannun mahaifana, na dawo hannun Hajiya Goggo. A lokacin mahaifina a cikin gidan nan yake zaune, nine jika na farko da su Mallam suka fara samu, ka san kuma ance abin cikin Kwan , ya fi kwan dadi, don haka suka dauki son duniya suka dora min, koyaushe ina tare da Mallam. Koda mahaifina ya kammala gininsa, zai bar gidansu, bai tafi da ni ba, a dailin hanin yin hakan da Mallam da Hajiya Gwaggo suka yi

Wannan shine asalin zamana tare da su, burin Mallam kuma a rayuwa shine kamar yadda na dauko kamanninsa, burinsa na gaje shi a fannin ilimi da Malanta, don haka tun Ina karamina Mallam ke koyar da ni karatun addini, domin Ina da shekara goma sha daya na sauke Alkur'ani. Malam da Hajiya sun fifitani fiye da duk wani da a cikin zuri'armu. Suna kaunata matuka, yadda ba sa kaunar ganin abinda zai bata min rai". Umar ya numfasa yace "To Muhseen yanzu mutanen dake nuna maka irin wannan kaunar, ashe har akwai abinda za su ce, ka yi ka yi shakkar yi? Har akwai umarnin da za su ba-ka, ka kasa bi? Haba Muhseen, yakamata ka yi tunani, don Allah kada ka watsa ma mutanan na kasa a Ido, domin idan ka yi haka, ka rage ma kanka daraja ne a gunsu, ai ina zaton ko cewa su kayi sun riga sun daura maka aure da wata bama Haneefa ba zaka hakura ka karbeta da hannu biyu balle ka duba karamcin da suka yi maka duk da abinda suke so ne su na kuma da damar da zasu ce dole kayi, amma haka suka baka zabi da damar kaje kayi tunani, na rantse da ni ne a matsayinka ko tashi bazan yi a gabansu ba zance na amince da bukatarsu”. Muhseen ya saki ajiyar zuciya yace "Ni kaina Umar ba na jin zan iya yin jayayya da su, na sami rauni a cikin zuciyata, na rasa mafita. Umar ina son na yi biyayya a garesu, amma ina tsoron fadawa hallakar Ubangiji, domin ina ganin idan na auri Haneefa, tamkar ba zan iya zama mijin kwarai a gareta ba, idan ko haka ne, ai ina ganin kamar ban ga amfanin yin biyayyar ba" Umar yace "Muhseen muna iya takura ma kanmu son abinda ba ma so, kuma mu so shi, mu kaunace shi, daga karshe. Saboda haka ka tursasa ma kanka son Haneefa, koda kwayar zarra ne, don Allah. Domin ina yi maka sha'awar auranta, ka ga hadin zumunci ne, kuskure kadan, zumuncin yana iya samun rauni. Don haka dole ka kiyaye Muhseen". Ya dago ya dade, yana kallonsa, kafin ya maida Idanunsa kasa. Hakika duk yadda Allah ya tsara maka rayuwa, ba-ka da yadda za ka yi, haka Allah ya tsara masa rayuwarsa, ba shi da matsalar