Page 35
komai sai matsalar abokiyar rayuwarsa, Amma anya Haneeta ta dace da shi? A gaskiya yana cike da tsoron zama surukin Hajiya Sa'a, duk da Goggonsa ce, to fa ba zai manta halinta na fada da naci da mita ba. Idan har Yarta ta shanye duk abinda zai yi mata, na rashin kyautawa, bayan auransu, Anya Hajiya Sa'a Ita za ta iya daurewa? Yana gudun duk wani abu da zai lya kawo matsala a cikin zumuncinsu, Shin tunda aure ake son yayi, me zai hana a daga masa kafa, ya kawo wata daga waje, koda baya sonta, ya aureta a bar maganar Haneefar. Wannnan tunanin yasa ya dubi Umar. Yace "Umar ni ina ganin me zai hana nace musu su bar maganar hadin zumuncin nan, su ba ni lokaci na kawo musu wata daga waje, Idan ya so sai na zaba a ciki *yan matan dake so-na, duk da ba sa gabana." Umar ya girgiza kai yace 'Kada ka fara wannnan tunanin Muhseen, na sanka ba-kada lokacin wata mace, kana tunanin za ka iya lalubo wata watan ma wacce zata ita jurar halinka? Don Allah Malam ka natsu, ka kama dahir, ka bi umarnin magabatanka, ka auri *yar'uwarka wacce ta sanka, ta san komai naka, wacce za ta so-ka ba don motar da kake hawa ba, ba don kudin da kake kashewa ba, ba kuma don gidan da kake cilki ba, sai domin Allah. Ka auri wacce za ta so-ka, so na auratayya, ta kuma so-ka, so na Yan-uwantaka. Yakamata ka bude idanunka sosai Muhseen. Rayuwa da lokaci ba sa jiran kowa, ka ci moriyar rayuwarka tun kafin ka ji ka a cikin kabari. Ban ga wanda ke gudun aure ba, balle wanda ke gudun dan-uwansa ba. Ba ka da dalili, ka san komai, me yasa kake ganganci da sanin da kake da shi?.” Maganganun Umar gaba daya gaskiya ne. Sun kuma ratsa zuciyar Muhseen kwarai. Ya juya yana kallonsa "Na gode Umar da fadakarwarka, ka tayani addu'a." "Na yi ma alkawari Muhseen, zan yi maka addu'a, domin rashin yin biyayya ga wandannan tsofaffin, tamkar KALUBALE ne a gareka." Daga nan falon ya kasance tsit! Dai-dai lokacin agogo ya buga karfe daya na dare. Daga nan Muhseen ya dan taba baccin awa biyu, domin karfe uku ya tashi ya fara gabatar da al'adar