Page 36
Rayuwarsa, wato sallar nafila, Shi kam Umar yana ta kwasar barcinsa. Washegari da safe Muhseen da Umar tare da Hajiya Goggo suka karya, Haka zalika Haneefa ce tayi ta dawainiya da bukatunsu, Umar ne kadai ke yaba mata, Domin tuni ya gane itace Haneefa, hakanan kuma ya ji ya yaba da ita, babu wani dalili da zaisa muhseen yace bai sonta , amma don Muhseen, duk irin hidimar da take yi tamkar ma ba don shi take yi ba. Domin ko a jikinsa. Boyan sun kammala karyawa ne. Suka wuce wajen Sheik sadisu Musa jigawa. Sun jima tare da shi, kafin su dawo su yi wanka, su shirya Zuwa daurin aure. Muhseen cikin wata hadadiyar shadda Ghalila me ruwan ganye , ya hadu , ko ba'a fada ba, sabon dinki ne. Ya murza hular da ta dace da kayan, haka takalmin da yasa duk sun dace da kalar kayan. A zahiri Muhseen ya tsera ma sa'a wajen iya shiga, ga shi duk kayan da yasa, sai sun yi masa kyau. Hakika ba banza ba 'yan mata ke macewa akan son dan mutan Jigawan ba, domin ya riga ya hada komai. Ga wata irin kamala da kwarjini na musamman da Allah ya hore masa, yadda duk yawan jama'a, Idan ya shiga cikinsu. Sai ya bambanta da su, saboda kwarjininsa na musamman, shi kansa Umar shigar Muhseen ba karamin burge shi tayi ba. Haka zalika ko a wajen daurin auran. Muhseen ya fita daban, ya zama abin kallo da sha’awa ga kowa. Bayan dawowarsu daga daurin aure. Haneefa ce ta shirya musu kayan abincin, domin dai ko ba komai, tana jin dadin yadda Umar ke nuna mata jin dadi, da yabawa akan duk abinda take yi musu. Ita ma tana sanye cikin wani bakin leshi ne, wanda ya dace da yanayin farar fatar jikinta. Haneefa ta lura kwarai da irin karbar karramawar da Umar yayi mata. Nan da nan ta ji jininsu ya hadu. Koda za'aje (Dinner Party)) din Hassan . Umar shine ya matsa ma Muhseen suka dauki Haneefa, ita kadal kuma suka dauka a motar tasu. Kujera ta musamman aka ba Babban Yaya tare da Umar da Haneefa. Ita kam Haneefa murna da jindadi ai ba' a Magana, burinta daya, shine su Bilkisu su ganta tare da Muhseen, domin su kore shakkar kaunar dake tsakaninta da Muhseen din, tana so su ganta don su gane abinda suka fada sunyi kuskure, tana kuma son ta kara musu haushi.