Page 37
To tayi matukar sa'a domin kuwa, duk masu Yi mata dariyar a daran jiya sun hangota kujera daya da Muhseen, wanda hakan ya janyo tsegumi a cikinsu, wasu na ganin su ne suka dace da shi ba Haneefa ba Masu haushi, na Ji masu yi mata murna da fatan alheri nayi Haneefa kam rabonta da shiga farin-ciki Irin na wannan dare har ta manta. Duk da dai ba wata cikakklyar magana bace ke hadata da Muhseen ba. Bayan an kammala (Party). Muhseen bai saurari komai ba, gida ya nufa. Haka zalika kai tsaye dakinsa ya wuce a matukar gajiye yake. Tare da Haneefa ya bar Umar. Haka zalika Umar din bai shigo ba har sai da Muhseen ya kammala wanka, ya kintsa, dai dai karte goma sha biyu da rabi na dare. Ya fito ya nufli dakin Hajlya Goggo, har ta fara barci. Ya tasheta. Ta yunkura ta tashi, tana kallonsa tace "Kun dawo Magajin Malam? “ Ya gyada kai yace "Mun dawo, ruwan zafi nake nema,ina son na dan sha shayi, babu wani abin kirki da naci tunda muka fita”.
Hajiya Goggo tace "To." Daidai lokacin Haneefa ta shigo dakin Hajiya Goggo, tana son ta kwanta ta dubeta tace "Yauwa Haneefa, talmaka ki hada ma Yayan ki ruwan shayi". Ta amsa da sauri, sannan ta shiga kokarin hada masa, sal da ta kammala tsaf! Sannan ta miko masa "Ga shi", Ya amsa a ciki yace "Na gode." Duk da a ciki ya amsa. To fa Haneefa ta Jidadi, domin wannan shine karon farko da tayi masa abu, ya nuna tayi masa. Yana kammala shan shayin. Ya mike yayi sallama da Hajiya Goggo, ya fice zuwa dakinsa. Umar na kwance kan kujera. Muhseen na shigowa, ya dube shi yace "Ina ka shiga ne mutumina? “Ya kwanta a kasan kafet yace "Ina wajen matata, na je na sha ruwan shayi ne." Umar yayi dan murmushi yace "M.U. Jigawa gaskiya yau Haneeta tayi kyau duk da ka ki yabawa mutumina, ka fa dace da mata." Ya juyo yana kallonsa. Yace "Umar na fahimci yadda kake kokarin cusa min ra'ayin a kan Haneefa, wanda ina tabbatar maka ba za ka cl wata riba ba, shawararka dai na dauka, zan daure na aureta. Amma batun ka cusa min sonta a raina, ba zai yuwu ba, ka kuma daina kokarin yin hakan."