KALUBALE BOOK 1

Page 38

by @yargidanimam

Umar ya dan gtada kai cikin dan murmushi yace "To ai anyi me wuyar tunda ka amince zaka aureta, so kuwa sannu a hankali zai shiga ina tabbatar maka kaima ba zaka san lokacin da zaka fara sonta ba, ni nasan wata rana zata samu kyakiyawan matsuguni a cikin zuciyarka." Muhseen ya lumshe idanunsa ya bude su sosai yace "Uhmmm Umar na gaji ina bukatar na huta barci zan dan yi kafin karfe uku." Umar yace "Kayi bacci lafiya “ Daga nan babu wanda ya kara Magana, kowa ya juya cikin tunani da sake-sake. Washegari muhseen yake shirin komawa Kaduna. Don yaso su wuce katsina gidansu Umar amma da yake mako daya kenan rabonsa da katsina yasa umar din yace ba zasu je ba don zasuyi dare a hanya don yasan babu yadda za’ayi su shiga katsina su fito akan lokaci .Karfe goma sha daya na safe suka kammala shirinsu .Muhseen Ya Iske Haj Goggo a dakinta, kusa da ita ya zauna, a tausashe yace "Hajiya mun kammala shirin komawa Kaduna." Tasa masa Ido tace "Magajin Mallam, me yasa ba za ka bari sai gobe ba,lokacin kaga an kammala komai na biki? Ya girgiza kai yace "Ni ma na so hakan, amma muna da aiki sosai gobe da safe, don haka dole na koma yau lahadi, don Idan nace zan bari sai gobe, to duk sammakon da zan yi nasan dole sai na makara". Tace "To shi kenan. Allah ya tsare hanya, kasan baxan bari ka yi wasa da aikinka ba." Ta tashi tana kallonsa "Bari na zo “. Ta shige uwar daki. Jimawa kadan ta fito, rike da wata bakar leda, ta zaua kusa da shi tana kallonsa sosai . Sannan ta mika masa ledar "Magajin Mallam ga wannan maganin,

maganin mutanan boye ne. Musamman na amso maka, saboda ina cikin damuwa, tan daga ranar da ka gaya min abinda ke damunka ban kara samun nutsuwa ba kullum ina cikin damuwa , don haka na amso maka, ko Mallam bai san na amso ba. Don ka san shi, sali ya hanani amsowa". Ido kawai Muhseen yasa mata, ta ci-gaba da cewa"Duk dare kafin ka kwanta, ka yi kokarin samun dan rushin wuta kadan, ka danki garin maganin, ka saka a cikin wutar, ka yi hayaki. To matukar ka yi haka, za ka daina wannan mafarkin da kake yi, zaka manta da wadannan mugayen idanun dake hana maka nutsuwa da ikon Allah domin za ka raba da aljanar da ta aureka" Muhseen yayi murmushi sosai yace "Ke kin yarda da cewa aljana ce ta aureni? Ta dan harare shi kadan, tace "To da waye ya aurekan? Kada ka ce za ka yi wasa da maganin nan, don Allah ka daure ka dinga y, don Allah. Kaji?” Muhseen Da “to “ ya amsa mata, domin ya san da zaran ya tsaya Jayayya da Ita, maganar nisa za ta yi. A dalilin hakan ya sa hannu ya amshi maganin .

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan imam KALUBALE BOOK 1 2009 Tsohuwar Ajiya Daga Habiba Abubakar Imam (Mrs Aliyu Mayere)

Bismillahir Rahma Nirrahim