KALUBALE BOOK 1

Page 39

by @yargidanimam

Ya tura a aljihun wandonsa ya kuma yi mata godiya, ita kuma tana kara nuna masa Muhimmacin maganin. Shi dai ya amsa mata ne kawai saboda ta jidadi domin dai shi da yake da kula’uzai da ayatul kursiyyu har me zai nema na tsari . Daga nan suka fito gaba daya har da Ita zuwa falon Shelk Sadisu, Shi ma din ya so muhseen ya bari sai gobe, amma da ya gaya masa uzirinsa, sai ya amince da shi. Sannan ya dube shi yace "Magajin Malam, a game da matsalarka, tun bayan komawarka na ke ta kokarn gano abinda ke faruwa na yi lya bincikena a game da mafarkinkan da kake yi,ni ma kuma Allah ya nuna min Idanun yarinyar da kake gani ,Amma Allah ya boye lamarinsa, domin ban fahlmci Komai ba a kan lamarin . Ban fahimci manufar mafarkin ba".Haj Goggo ce ta gyara zama tace "A'toh Na ce muku shafar aljanu ne,amma kun ki yarda da maganata". Sheik sadisu ya Ya daga mata hannu, yace “Don Allah ki bar wannan maganar domin har yanzu ina nan akan bakata na cewa babu wani aljanu, illa dai akwai wani abu da ubangiji yake son ya nuna wanda bamu isa mu san ko menene bane ,har sai lokacin da Allah ya so hakan, don haka muyi ta addua kawai” Haj Gwaggo tayi shiru. Sannan ya dubi muhseen yace "saboda haka kaima ka kara dagewa da addu'a kamar yadda ka saba, ina kuma kara jaddada maka maganar Haneefa, ka tabbatar ka share manà hawayenmu a taro me zuwa." Muhseen ya gyada kai yace '"In Allah ya yarda". Sheik sadisu yayi murmushi yace "Allah yayi maka albarka". Dukkansu suka amsa da amin. Daga bisani su ka yi sallama, bayan muhseen ya aje musu kudi kamar yadda ya saba ,sun sa masa albarka shima kamar ko yaushe, sannan Muhseen ya fito, shi ma Umar yayi sallama da kowa hade da godiyar irin karamcin da aka yi masa, ba su yi sallama da Haneefa ba, a dalilin bata gidan, ba tayi zaton yau muhseen zai koma ba, da tabbas babu inda zata je sai taga tafiyarsu.kuma Umar bai so haka ba. Ya so su yi sallama, shi ko Muhseen ko a Kwalar rigarsa. Bai damu da rashin yin sallama da Haneefar ba. Da ganan suka kwashi hanya umar na cike da santin yanayin rayuwar gidan sheik sadisu. Muhseen Usman Jigawa ya ci-gaba da maida hankali akan aikinsa, ya daure ya ki yarda halin da yake ciki ya shafi aikinsa,duk da yana cikin damuwa, sai dai jarumtarsa da boye abu a cikin zuciyarsa yasa babu wanda ke gane halinda yake ciki,idan aka cire umar da ya roga yasan komai kuma kullum karfafa masa guiwa yake yi akan yabi umarnin magabatansa.wanda Zuwa wannan lokacin tuni ya amince ma kansa cewa zai iya auren Haneefa.domin yin biyayya ga magabatansa, ba don so ko kauna ba, haka zalika har zuwa wannan lokacin, jefi-jefi yanayin mafarkinsa daya riga ya saba da shi. Ya kuma zamar masa jiki. Domin dai har yanzu baiyi amfani da maganin da Haj Gwaggo ta bashi ba,saboda tun da ya dawo daga jigawa ya jefa shi a cikin durowa bai kara bi ta kansa ba. Ya riga ya bar ma Allah komai duk kuma yadda yayi da shi dai dai ne.