KALUBALE BOOK 1

Page 40

by @yargidanimam

Hajiya Sa'a dai ta sanya buri akan auran autarta Haneefa da Muhseen, bata zaune, bata tsaye. Ta shiga gidan wannan dan-uwa, ta shiga Gidan wancan, tana cusa musu ra'ayin auran Haneefa da Muhseen. Yauma tun safe ta fita tana gidan mahaifin Muhseen tare da Hajiya Hadeeza Maganar suke, gaf Da za ta tafi ne. Sagiru dan wajen Alhaji Sani ya shigo gidan da (Ghana most go), na kaya. Bayan ya gaidasu ne, ya mika ma Hajlya Hadeeza Jakar kayan yace "Ga shi, Hajiya Goggo tace a kawo miki, wai sako ne daga Yaya Muhseen a raba ma duk wanda ya dace." Hajlya Hadeeza gyara zama fuskarta na bayyanar da jindadin ta,tace "To,aje su anan in sha Allah za’a ba duk wanda ya dace ,ka ce ina gaidata." Daga nan ya fice yana tafiya. Hajiya Sa'a tayi wuf ta janyo Jakar, ta bude "A'a ai kaya ne Hajiya, atamfofi da shaddoji , lalle Muhseen baya gajiya Allah ya kara arziki “ Hajlya Hadeeza tayi murmushi tace "Ai haka ake so Hajiya, Idan ka sami wadata, wani ya karu da kai, duk wanda zai samu arziki bai taimaka ma masu bukatar taimako ba ai arzikin nasa baida amfani” Haj sa’a tace “Gaskiya ne, amma duk da haka dai muhseen da ban yake , abunda yake yi ba duk mutum ba, yana kokari sosai”. Nan dai tayi ta yabon muhseen har sai da Haj Hadeeza ta ji kamar duk duniya babu wacce ta kaita sa’ar samun da nagari . Daga bisani Haj sa’a ta yunkura za ta tafi. Nan da nam Hajiya Hadeeza ta dakatar da ita. Ta tashi ta dauko leda, tasa mata shadda da atamfa tace "Ki ba Mallam shaddar, atamfar kuma ta ki ce". Sannan tasa wasu atamfofin guda biyu tace "Wannan kuma na Haneefa ne, ta kai a dinka mata, don Allah". Dama abinda take so kenan. Nan da nan ta cika da fara'a tace "A'a Hajiya, ai duk mun kwashe kayan. To Allah ya saka da alheri, an gode". Tace "Ameen". Har bakin kofa tayi mata rakiya, sannan ta tafi. Gaf Da za'a kira sallar magariba. Hajlya Sa'a ta shiga gida. Mallam Jibrin na zaune, da butar alwala a gabansa, yana jiran a kira sallah, tunda ya amsa mata sallamar. Ido yasa mata har ta wuce, tana kwala ma Haneefa kira. Ta fito da sauri tana fadin "Hajlya, sai yanzu? " ta amsa “Eh, miko min tabarma na zauna. Na kwashi Iskar wajen nan, wannan zafin yayi yawa." Da sauri Haneefa ta fito da tabarmar, ta shimfida, gaba daya suka zauna. Hajiya Sa'a na maida ajiyar zuciya, Malam Jibrin ya numfasa cike da takaici yace "Yanzu Sa'a ki fita gidan nan tun safe, sai yanzu ki ke dawowa? Babu abinda ya dameki, kin ko san darajar aure? Ki fita ki bar gidan mijinki, babu tunanin komai. Tsakani da Allah. Ya’ya mata ke gabankl, da haka ki ke son su taso?..... bata bari ya kai karshen maganarsa ba.