Page 41
Ta katse shi "Ka daina yi min irin wannan mummunan fatan. 'Ya'yana da tarbiyyar kwarai suka tashi,sun san fari sun san baki,kuma fita da nayi sada zumunci bashi da wani aibu,don haka ina fatan su gado ni awannan halin da kake kushewa,”. Ya girgiza kai yace "Ki daina fadan son ranki, Sa'a bari ki ji, ko awa biyu ba'a rufe ba, da Musa surukinki mijin Sameera ya bar gabana, ba ki kuma san abinda ya kawo shi ba? Kara ya kawo min akan dabi'ar da yarki take a gidan auranta, ta raina shi, bata girki, ga fita anguwa, ga wulakanci da Izgilin da take yi masa a gaban kowa. Ya gaji, shi yasa ya kawo min kararta, don Allah aja mata kunne". Hajiya Sa'a tasa masa ido tace "To me ka ce masa?" ". Ya nisa yace “Me zance masa, daya wuce na ba shi hakuri, tunda duk abinda ya lissafo, ke ma uwarta haka ki ke yi min. Wannan mummunan koyi ne daga gareki, za kuma ki gurbata zaman auran 'Ya'yanki ,to saura Haneefa, tunda Ita ma abinda ta ga ki na yi min, shi za ta Yima mijinta. Sai dai Allah ya kyauta." Nan da nan Hajiya Sa'a ta fara fada 'Shi Musan ya gama gulma da kinibibinsa? Dama niya samu. Daya sha mamaki, don rainin arziki da can bai san Sameeran na yi masa haka ba, sai yanzu? Ina ma laifi da ta aure shi. Alhalin ba shi da ko sisi, bai aje ba, bai ba wani ajiya ba. Ni idan ba zai iya ba, ya sako min 'yata mana, ni ba na son jaraba,da rashin hakuri,gami da shegen korafi irin nasa”. Jin yadda ta fitittike da fadanta na tsiya, yasa nan da nan Malam Jibrin yayi gagawar Idar da alwalarsa, ya fice daga gidan, don ya san karshenta ya dawo kansa fadan nata, tunda ba wai tana ganinsa da gashi ba ne. Yana fita, ta dubi Haneefa tana hucin fusata tace "Ki na nan Musan ya zo? “Ta daga kai "Ina nan." "Me Babanku yace masa, nasan ya fadi magana a kaina ko”Haneefa ta gurgiza kai tace “Hakuri yayi ta ba shi, kamar wanda yayi masa wani gagarumin laifi, yace kuma zai je har gida ya sami Yaya Sameeran, sai ya bata mata rai", Hajiya Sa'a ta saki tsaki tace "Aikin banza. Allah yasa wata rana yayi gangancin kawo min karar Sameera, sai ya gane kuransa". Daga nan Haneefa ta janyo jakar ledar kayan tace "Hajiya, me ki ka taho mana da shine?” Tayi murmushi tace a yayin da take dauko atamfa turmi biyu, ta dora mata akan cinyarta tace "Na ki ne wannan autata, surukarki Haj Hadeeza tace na kawo miki