Page 42
Muhseen ne ya aiko da su a rabama duk wanda ya dace, shine Allah ya tsaga da rabon mu, ina gidan aka kawo, shine ta ba ni, harda babanki shima ya samu shadda me kyan gaske, kin ganta”.
Ta dakko tana nuna mata, Haneefa ta kara cika da fara’a tace “Lalle baba ya morema shadda, baisan haka ba yake ta fada kinje kin zauna,amma dai mun gode”Haj sa’a ta tabe baki tace “Rabu da shi kinji, muyi abinda ke gaban mu”, ta kara gyara zama tace “ kin samu karbuwa a wajen Haj Hadeeza sosai, ina ji a jikina autenki da muhseen babu fashi, haka zalika auran naku ba karamar nasara ba ce, don nasan in dai ya aure ki ni ma dole ya dinga aiki min da irin wadannan kayan “.
Ta kara gyara zama ta cigaba da cewa “ nasan yadda yake hidimta ma mahaifansa ni ma haka zai dinga hidimta min , kinga dai yanzu babu wata matsala domin gaba daya yan’uwa sun amince uwa uba su Haj Gwaggo da Mallam sun yarda tuntuni nasan kuma ko dan su babu yadda zaayi muhseen yace bazai aure ki ba, na san tabbas a taro na gaba zamu samu hadin kansa” Cike da jindadi Haneefa ta daga hannu tana ma Allah godiya.
Za tayi magana kenan Mallam Jibrin ya shigo ko kallonsu bai yi ba,ya shige dakinsa. Haj sa’a ta tabe baki, ta mika ma Haneefa shaddar tace “ je ki ki kai masa idan yana so, ki gaya masa muhseen ne ya aiko masa da shi”. Ta amsa lokaci daya ta ta nufi dakin nasa, bayan ta kai masa ya karba ba yabo ba fallasa, domin har yanzu cikin damuwa yake ,duk duniya bai da wata damuwa da ta wuce ta Haj sa’a.
Tun saura kwanaki biyu Muhseen ya je jigawa taron su ya sami kansa cikin kunci da matsin zuciya. Duk da ya amince da auran Haneefa amma har yanzu baya jindadin zuciyarsa . Don ma ya sami umar yana kwantar masa da hankali, domin ko tafiyar da zaiyi ba don umar din shi ma zai wuce katsina ba yaso su tafi tare.