Page 43
Dole su ka yi sallama, kowa ya kama hanyar mahaifarsa. Yau dai Muhseen ya ba kowa mamaki, domin babu wanda ya jira shi a wajen taron. Asalima ya riga wasu 'yan garin halartar taron akan lokaci, domin sammako ya bugo, duk don ya burge mahaifinsa, ya kuma tserar da Sheik daga korafin 'ya'yansa a kansa. Lalle kam! Domin dai Sheik Sadisu ya ji dadin ganin Muhseen akan lokaci, tamkar zai maida shi ciki. Saboda kauna, kusa da shi yayi zamansa. Cikin kankanin lokaci falon ya cika, kowa ya halarta. Daga nan aka bude taron da addu'a. Sannan sun yi ma juna godiya a bisa hadin kai da gudunmawar da kowa ya bayar a bikinsu Hassan. Sannan aka sako maganar da tafi kowace magana muhimmanci a wajensu, wato maganar auran Muhseen da Haneefa, wanda nan da nan Hajiya Sa'a ta kara gyara zamanta, ta tsire Muhseen da fitinannun idanunta, yadda ko yaya ya dago zai ganta. Sheik Sadisu yayi yar gyaran murya yace "Maganar auran Muhseen da Haneefa na ba shi lokaci yayi tunani, domin ko mun matsu yayi aure, ba shi zai sa mu yi masa dole ba. Amma ina son ya san cewar matukar zai bi son ranmu ne, da abinda zukatanmu suke so. To Haneefa ita ce matarsa, domin muna so, mun kuma yi na'am da hakan, don haka ina fatan duk tunanin da ka yi, bai wuce irin tunanin da mu ma muka yi ba?”. Daga nan yayi shiru, yana dubansa, sannan yace "Duk muna sauraranka mu ji hukuncin da ka yanke?”Cikin taushin murya da saduda Muhseen yace “Malam, na amince, na yarda zan auri Habeefa, Allah yasa hakan Shine ya fi zama alheri". Hajiya Sa'a ta runtse idonta , cike da farin-ciki, tana yima Allah godiya a cikin zuciyarta. Su ma duk wadanda ke falon cike suke da mura. Musamman Alhaji Usman. Yau dai Muhseen ya fitar da su kunya. Nan da nan falon ya kaure da surutan murna da farin-ciki. Bayan sun natsu ne. Sheik Sadisu yace "To Allah yayi maka albarka, dama na san ba za ka taba ba mu kunya ba, don haka magana ta kare, ba wani dogon lokaci za'a dauka ba. Amma yana da kyau ku kara fahimtar juna kafin daurin auran."
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan Imam KALUBALE BOOK 1 2009 Tsohuwar Ajiya Daga Habiba Abubakar Imam (Mrs Aliyu Mayere) Bismillahir Rahma Nirrahim