KALUBALE BOOK 1

Page 44

by @yargidanimam

Muhseen ya gyara zamansa Yana shirin yin magana kenan Haj sa’a ta amshe "Ai Haneefa ba bakuwar muhseen bace da zasu bukaci lokacin kara fahimtar juna, babu komai Mallam in sha Allah wannan auren zai zama abin alfahari a gare mu”, sheik sadisu yace “Duk da haka dai yana da kyau a basu damar kara fahimtar junan su”, zata kara magana ya daga mata hannu yace?” Kinga sa’a bana son musun ki na tsiya, abar maganar nan haia “. Dole yasa ta bi umarninsa ta yi shuru, tunda dai burinta ya cika ai shikenan. Daga nan kowa ya cigaba da fadan albarikacin bakinsa har zuwa lokacin da taron ya tashi. Wanda rabon da ayi irin wannan taron mai dadi har an manta. Bayan tashi da ga taron babu wanda ya kara ganin Muhseen, domin yana cikin dakinsa ya kulle da makulli. Kowa ya zo zai shiga dakin da tunanin yana ciki sai ya koma, Ya dauka ko baya ciki ne. Ita kanta Hajlya sa’a zuwanta kofar dakin sau uku, tana dawowa, tana son ta gan shi, su yi Magana, amma har lokacin tafiyarta yayi,ba ta ga Muhseen ba. A dalilin hakan ta sami Hajiya Goggo ta zauna kusa da lta tana kallonta ,Hajiya Goggo tace "Menene kuma? Ko akwai sauran wata fitinar ta ki ne?, Ba an riga an gama maganar ba, kuma yanzu menene?”. Ta girgiza kal tace "Ba wani abu bane, don Allah Hajiya Ina son naga Muhseen ne,akwai maganar da nake son yi da shi, amma na rasa Inda ya shiga". Haj Gwaggo ta ce"To ni ma ai ban san inda ya shigan ba, ni ma nemansa nake yi ya zo ya ci abinci “. Tace "To ali shine zan bar miki sako, tunda ke na san dole kl gan shi." Hajiya Goggo tasa mata ido, tace 'Wane sako ne? Ta dan gyara zamanta tace “ ki Ce masa lalle ya zo gida ya sameni, ina nemansa. Kada ya sake ya koma ba tare daya zo ba, don na san yana iya tafiya bai zo ba. Wannan shi ya fi komai sauki a gunsa". Hajlya Goggo ta kauda kai tace "Ni Sa'a ba na son kwazzabar ki ta tsiya. Amma shi kenan zan gaya masa, zal kuma zo.Shi kenan ko? “ Ta tashi tana sanya hijabinta "Shi kenan Hajiya, ni na tafi gida, kada wannan sarkin yan korafin yace na dade." Hajiya Goggo ta tsareta da ido tace "Wa kenan". "Malam mana". Ta bata amsa a gajarce Hajlya Goggo ta fiddo Idanu waje cike da fushi tace "Ashe ba ki da hankali Sa'a. Mijin naki ne ki ke ce masa Sarkin korafi? Ki na son ki gama lafiya kuwa? Miji, ai ya fi karfin wasa da raini. To ki Kiyayi kanki, kada ki ci wuta". Hajiya Sa'a ta bata fuska tace "Yi hakuri, sai anjima". Ta fice da sauri Haj Goggo ta bi ta da harara, tana mamakin furucinta. Lalle Hajiya Goggo bata san halayyar yarta ba, da ta sani, wannan ba wani abin mamaki bane. Don kawai tace "Sarkin korafi". Domin Tana fadan ma abinda yafi wannan muni, tana yi masa tijarar da tafi wannan, don dai Mallam Jibrin me hakuri ne, yana kuma ganin darajar Sheik Sadisu a matsayinsa na surikinsa. Kuma Malaminsa, domin a dalilin karatun da yake dauka a wajensa ne.