Page 45
Allah ya hada shi da Hajiya Sa'ar, don haka dole ya zama me hakur tare da kauda kai, akan munanan halayanta. Da ta ara, ta yata ma kanta, domin dai Malam Jibrin ya san ta sami sahihiyar tarbiyya a wajen mahaifanta. Daga baya ne ta yar da tarbiyyar, ta dauki rayuwar da take so, wacce tayi mata. Sai bayan sallar magariba. Sannan Muhseen ya fito, wanda zuwa wannan lokacin ba Hajiya Goggo ba, hatta Sheik Sadisu ya damu da rashin ganin gilmawan gudan jinim nasa. Muhseen yana shiga dakin Hajiya Goggo. Tayi wuf! Ta dago tana kalionsa tana fadin "Magajin Mallam , ina ka singa, don Allan ina ka je?” Ya zauna kusa da ita, yana cewa 'Ina dakina Hajiya, na kulle kaina saboda na samu na huta, na yi dan barci". Ta saki ajiyar zuciya tace "Amma ai sai ka sanar da ni ko?”, yayi dan murmushi yace "Na yi kuskure ayi min afuwa". Tayi murmushi tace "Ya wuce, ya maganar abinci? Ga shi can daga wajen matan Sani aka kawo maka, ga kuma wani can sai ka zabi wanda kake son ci". Ya lumshe ido, ya bude yana kallonta yace "Ba ni kowanne zan ci". Ta tashi ta dauko masa abincin ta zuba, ta mika masa, ta koma gefe ta zauna, tana kallon yanayinsa. Cikin rashin kuzari da alamun damuwa Muhseen ya dan ci abinda zai iya ci. Sannan ya koma ya kwantar da bayansa a jikin kujera. Hajiya Goggo ta kasa jurewa, don haka tace tana me dubansa "Magajin Malam, damuwar me nake gani a fuskarka? Ya girgiza kai "Ba na cikin damuwa Hajiyata." "Ka daina fadan haka, domin na sanka kamar yadda na san kaina, damuwanrka ba za ta taba boyewa a gareni ba, kana cikin damuwa mana, menene" Muhseen ya numfasa yana kallonta. Sannan yace "Hajiya, ina guje ma kaina fadawa hallaka ne". "Kamar yaya?" Ta tambaye shi, yayi shiru na dan wani lokaci sannan yace "Kun tilasta min auran Haneefa. Alhalin kun fi kowa sanin halin da nake ciki. Hajiya haka zan aureta na zauna da ita, ba na sonta, ki na ganin zan iya yin adalci a gareta? Alhalin ba na sonta? Na san girman aure, na san darajarsa, don haka nake jiye ma kaina tsoron fadawa hallaka. Hajiya ina jin tsoro."