KALUBALE BOOK 1

Page 46

by @yargidanimam

Cike da tausayi Hajiya Goggo ta matso kusa da shi sosai, ta dafa saman kansa tace 'Kada ka damu, wannan dalilin yasa na ji ina da matukar sha'awarka auri Haneefa, domin 'yar-irwarka ce. Ita ce dolenka, ita ce za ta iya rufa maka asiri, ta boye sirrin zamanku, don haka ka daina damuwa, watarana na tabbatar za ka so Haneefa. Nasan kuma duk runtsi ba zaka iya wulakanta mace ba balle matar ka, ina da yakinin cewa zaka yi ma Haneefa adalci, Allah kuma zai cire maka rashin son mata, za ka ji dadin zaman aure Magajin Malam." Ya dubeta sosai yace 'Kin tabbata Hajiya". "Ya tambaye ta yana kafeta da ido . Ta muskuta tace “ Ba ni da tabbaci, domin bansan gaibu ba, sai dai nasan babu abinda ya gagari Allah. Addu'a kuma muna nan, mu na yi, ba na tsammanin Allah zai juya ma bukatunmu baya, biyayyar da ka yi mana kuma Allah zai tabbatar da farin-ciki a rayuwarka, ka daina sa ma kanka damuwa, gara ka yi auran, domin zama ba aure ba zai taba yuwuwa ba. Domin duk martabarka, matukar ba kada aure, ba kada wata martaba. martabarka auranka. Allah ya tsareka daga kowane irin sharri" A sanyaye yace "Ameen Hajiyata nagode ". Ta nisa tana dubansa, tace "Yaushe za ka koma?" Yace "Gobe nake son komawa Hajiyata." Tace "Allah ya kaimu, amma kafin nan. Goggonka Sa'a na nemanka dazu. Tayi ta zaman jiranka, har lokaci ya kure. Ta hakura ta tafi, shine tace na gaya maka ka je ka sameta. Akwai maganar da za ku yi". Cikin rashin son hakan ya kara lumshe idanunsa, ya bude yace "To zan yi kokarin zuwa yanzu, domin gobe babu lokaci tunda da safe nake son tafiya". tace "To duk dai daya". Daga nan ya dubi agogo takwas da kwata, don haka ya mike yace "Hajiya bari na amsa kiran Goggo". Tace "To, sai ka dawo, kada kuma ka shantake a can". Yace "To matas". Daga nan ya fice da sauri. Muhseen na tsaida motarsa a kofar gidan Malam librin, ya hango Malam Jibrin din zaune akan tabarma da yara matasa a gabansa, suna daukar karatu. Cikin girmamawa Muhseen ya karaso gunsa, har kasa ya durkusa ya gaida shi. Cikin kauna da kulawa Malam Jibrin ya amsa masa, sannan ya tashi ya shiga cikin gidan, albarkacin wutar Nepa gidan yayi haske tamkar ba dare ba, yana yin sallama. Haj Sa'a tayi wuf! Ta dubi Haneefa tace “ ga muhseen nan yi sauri ki yi yar kwaskwarima, ki shafa hoda kinga akwai hasken nepa ,zai ga fuskar ki sosai”