KALUBALE BOOK 1

Page 47

by @yargidanimam

Haneefa ta tashi da sauri ta fada uwardaka. Daidai lokacin Muhseen ya shigo falon cike da fara'a. Hajiya Sa'a tace "Muhseen shigo mana, ashe kana tafe? “Ya karaso ya sami kujera ya zauna ya gaidata, ta amsa. Tsawon lokaci sannan yace "Hajiya ce tace ki na kirana, shine na zo". Tayi dan murmushi tace "Eh, anyi haka". Ta dan gyara zamanta, gami da kwala ma Haneeta kira, ta amsa, lokaci daya ta fito daga daki. "Kawo ma yayanki ruwa." Muhseen yay saurin cewa "A'a Goggo, babu abinda zai iya shiga cikina, a koshe nake da komai". Haneefa ta durkusa ta gaishe shi, ya amsa mata cikin sakin fuska. Daga nan Hajiya Sa'a ta dubeta tace "Je ki, ki ba mu damar yin magana". tace "To". Lokaci daya ta juya ta koma cikin daki. Hajiya Sa'a ta dubi Muhseen, tace "Muhseen, dalilin kiranka, abu daya ne. Amma me muhimmanci ne, ina ganin ko babu maganar aure tsakaninka da Haneefa. 'Yar-uwarka ce, za ka iya yi mata komai, ba tare da bacin rai ko rashin jin dadi ba.” Muhseen ya dago ya dubeta yace "Goggo, duk ina maganar ta dosa ne? Yakamata ki gaya min kai tsaye kawai." Hajiya Sa'a tace "Tunda ka amince za ka aureta, ina ganin ai ya zama dole na gaya maka." Tayi shiru tana kallonsa, sannan ta Cigaba da cewa "Akwai wani yaro da ,daya so Haneefa, amma tunda na furta kai zan ba Haneefa, Yaron ya shiga damuwa. A takaice dai har ta kai na gaya masa ba ruwansa da ita. Kada ya kara zuwa wajenta, to zafin hakan ne yasa yace duk abinda ya kashe ma Haneefa, sai an biya shi. To a gaskiya ya kashe ma Haneefa kudi, ba kuma zan iya biyansa ba. Kamar yadda na san Babanta ba zai iya ba, tunda babu abinda yake da shi a ajiye ko a cikin aljihunsa, don haka na ga kai ne yakamata ka biya kudin. Tunda kai ne za ka aureta, kuma Allah ya hore maka, dalilin da yasa nace ka zo kenan" Ran Muhseen ya dagule, a hankali yace "Goggo da, kin san akwai wanda Haneefa take soyayya da shi, amma k ka kawo maganar aurena da ita? Ta dan gintse fusta tace "To meye? Da bare, ai gara dan gida, kai hankalina ya fi kyranciya dana ba