Page 48
Haneefa, domin ina da tabbacin a hannunka za ta ji dadi sosai. Sai dai kuma idan kana ganin ba za ka biya kudin ba to shikenan babu damuwa Amma kada ka kawo wata Magana,wai me yasa ba’a ba Haneefa shi ba. " Ya numfasa yace cike da jin haushi "Ba haka bane, nawa ne kudin? “ Haj Sa'a ta karkace tace "Naira dubu dari ne, a iya lissafin da yayi” Muhseen yace "Dubu dari? "Eh, haka yace". Yayi shiru zuwa wani lokaci, yace "To ki yi hakuri, a yanzu ba ni da wadannan kudin. Amma idan na koma, zan aiko miki da su. Shi kenan? Tayi murmushi tace "Shi koan, an gode. Allah ya kara arziki, kaga shikenan sai ya bi wani sarkin kuma”Yace "Amen, bari na koma, don gobe da safe nake sa ran barin garin". Ta kara murmusawa tace "To Allah ya tsare hanya'. Ya tashi, dai-dai lokacin ta kvala ma Haneefa kira "Haneefa ki fito kiyi sallama da yayanki kiyi masa rakiya". Da sauri ta fito, wanda duk da haka. Muhscen har ya kai zauran gidan. Anan ya ja ya tsaya, yana jiran ta karaso. Yana tsaye. Haneefa ta iso ta tsaya a gabansa, ya dade yana kallonta, sannan yace "Hannefa idan ba ki da ra'ayi a kaina, kada ki zalunci kanki, ki fito fili ki fada? “Ta kafe idonta a kansa, tace 'Me yasa ka yi wannan maganar?” Yace cikin rashin sakin fuska "Saboda ki na soyayya da wani, wanda nake ganin kun yi dadewar da bai kamata ace kin yaudare shi ba, domin da ba ku dade tare ba da bai yi miki hidimar kudi har na Naira dubu dari ba. Yaudara, babu kyau. Idan kin san har yanzu ki na sonsa, to ki gaya min, sai a warware komai cikin sauki". Hankalin Haneefa ya tashi, ya za ta yi ta iya gaya ma Muhseen karya mahifiyarta take yi? Ta dan dube shi, tace "Yaya Muhseen, ka bar wannan maganar, domin kai kadai nake so, kai kadai nake kwadayin na yi zaman aure da shi. Ina kaunarka...”. Ya katseta ta hanyar daga mata hannu "Shi kenan, nagode da kaunar, ki koma gída". Ta tsaida idanunta a kansa tace "Ni ma na gode. Allah ya tsare hanya',. Ficewa yayi, ba tare da yace komai ba. A waje sallama yayi da Malam Jibrin, ya dauki hanyar gida. Zuciyarsa cike da tunani. "Anya auransa da Haneefa zai zama abin alfaharin dangi? Anya ba za'a sami matsala ba? Hakika yana tsoron halayya da dabi'un Hajiya Sa'a. Auran zumunci kuwa yana bukatar juriva da taka tsantsan! Cikin wannan tunanin ya isa gida, haka zalika bai gaya ma