KALUBALE BOOK 1

Page 49

by @yargidanimam

Hajiya Gwaggo komai ba a game da kiran da Hajiya Sa'a tayl masa. Ita ma kuma ganin bai gaya mata ba, yasa bata tambaye sil ba. Fuskar Haneefa a turbune ta shiga dakin Haj Sa'a,tana kallon ta cike da tuhuma Haj sa’ata dubeta tace "Har ya tafi? "Ta ce “Ya Tafi amma Hajiya, banjidadin maganar da kika gaya masa ba, gashi nan har yana tunanin ba shi nake so ba, kuma kinsan duk abinda ki ka fada masa ba haka bane, to me yasa zaki fada”

Ta dan harareta tace "Kada ki yi min gurguwar fahimta, sanin kanki ne babu abinda ki ka ci a wajensa, kuma ba wani lokaci za'a dauka ba, za'a daura auranku. Kenan haka za ki aure shi. Babu ahinda muka samu daga hannun shi? Kuma kin san cewa Mahaifinki ba shi da weni karfi, batun kayan dakinki, daga ni sai Yan-uwana. Don haka kin ga dubu darin nan, ba karamin taimakonmu za ta yi ba.... "Sa'a ki ji tsoron Allah kullum. Ni a matsayin matsiyaci ki ke daukata, wanda ba zai iya tsinana ma Ya'yansa, komai ba, kuma kin san karya ki ke, ki ce ba na yima Ya'yana komai, in auransu ya tashi. Amma rainuwarki ta tsiya da hange-hangenki suke hanaki ki ga bajintata."

Cewar Mallam Jibrin, cikin fusata yana tsaye a bakin kofa. Hajiya Sa'a ta gintse fuska tace "To sai ka gaya min abinda kake tsinanawan, da duk abinda zan yi idonka da kunnanka na kai Saboda kana kokarin ka lika min magana".

Malam Jibrin yace "Ki bar cika bakin banza. Haneefa dai Yata ce, ba yar mace ba, idan ki ka yi wasa, ki ka kuma tukeni, na rantse ina iya cewa ba zan ba Muhseen ita ba. Kin san kuma na isa" Ta gyara zamanta tace "Dama magana kake nema, shi kenan a bar maganar. Allah ya ba-ka hakuri". Ya saki tsaki gami da: juyawa a fusace, ya shiga dakinsa. Hajiya Sa'a ta dubi Haneefa, ta ja tsaki tace "Ke ba ki da hankali, don kawai na amshi dubu dari a hannunsa, shine ki ke tambayar ba'asi? Ga shi nan wannan dan sa idon ya ji, meye dubu dari a wajen Muhseen?Ko An gaya miki kananan kudi ne gare shi? To ki shiga hankalinki, domin ko anyi auran da irin wannan karyar, za ki dinga