KALUBALE BOOK 1

Page 50

by @yargidanimam

yagar rabonki a wajensa, babu wani tausayi a tsakaninku, domin Muhseen ya riga ya tara kudi fiye da tunaninki." Haneefa ta rausayar da kai gefe, tace "Shi kenan, Haj na fahimce ki”. Irin maganganun da Hajiya Sa'a tayi ta yima Haneefa, kwata kwata bai kamata ace duk uwar kwarai tana yima 'yarta ba. Allah ya kyauta, Washegari Muhseen da wuri yayi sallama da kowa. Ya kama hanyar Kaduna. Bayan mako daya da dawowarsa, ya aika ma da Hajiya Sa'a Naira dubu darin da ta nema. Murna da zumudi a wajenta, ai ba'a Magana, ta sami dubu dari a sama, domin dai ko tasa ba za ta sai ma Haneefa ba, don ta san Yan-wanta ne za su yi komai. Za ta kara jarl akan Jarinta na da. Babu wanda ya sani. Maganar biki ta tashi gadan -gadan, sai dai Muhseen ya nemi alfarmar a daga masa kafa, domin ya samu ya kammala gininsa daya fara anan Jigawan. A dalilin hakan aka yi shiru da maganar bikin. Muhseen ya cl-gaba da aiko ma da kanin mahaifinsa Alhajl Sani kudin ginin, domin dama shi yasa a gaba a aikin, domin yana da amana sosai. Gidan Muhseen na jigawa nan kusa da gidan Sheik Sadisu yake, kusa nev sosai domin filin na sheik sadisu ne ya bashi tuntuni,daga ka fito daga gidan sheik sadisu sai gidan Muhseen, kasancewar da "filin ma a cikin gidan yake. Daga bisani Bayan ya mallaka ma Muhseen din, shine aka katange, aka fitar da shi, daga cikin gidan. Ginin da yake yi me kyau ne da kyan tsari. Duk da kasancewar karami ne. Amma yana da matukar ban sha'awa sosai. Ta bangaren Haneefa kuwa, ta rasa inda auran na su yasa gaba, domin har zuwa wanan lokacin da aka gama maganar auransu, sam! Muhseen baya nuna damuwarsa a kanta, har yau bai taba cewa yana sonta ba, har yau bata taba daukar awa daya suna hirar ba, balle fa su fahimci juna, domin ko zuwa yayi. Kamar yana dibar wuta, babu wani sakin fuska a tsakaninsu, duk da dai ta san wannan halinsa ne, ba kuma za a iya ¡Canja shi ba. 'Sau tari sai dai ta kira shi a waya, kuma abinda yake Bata mata rai kullum ta kira, sai ya tambayi me Magana, saboda tsabar wulakanci.

Ku dakace ni

Daga taskar

Yar gidan Imam KALUBALE BOOK 1 2009 Tsohuwar Ajiya Daga Habiba Abubakar Imam (Mrs Aliyu Mayere)

Bismillahir Rahma Nirrahim