Page 51
Hakan yake tabbatar mata da cewa Muhseen ba shi da lambarta a wayarsa. Dama ita ma wajen umar ta amshi lambarsa, duk da haka Haneefa bata nuna masa damuwarta ba, ta’aje, ta adana komai,sai ranar da ta zama mallakinsa, sannan tayi alkawarin taka masa birki. Domin a lokacin ne za ta nuna masa ainihin kalarta, domin ba zai yuwu ta zama a bar wulakantawa ba a wajen namiji. Dole ya so ta, dole ya damu da ita, kuma dole ya bauta mata. Wannan alkawarinta ne, domin ba za ta so shi a banza ba, ta san abinda take yi. Ya zama dole ya canja halinsa, idan ba haka ba kuwa, lalle za ta zamo masa babban KALUBALE
Cikin watanni hudu cikin na biyar. Muhseen ya kammala gininsa, Inda yake son aje matarsa. Haka zalika makwanni blyu tsakani, aka kai sadakin Haneefa hannun Malam Jibrin, kamar yadda suke so. Malam Jibrin bai ja wani lokaci ba. Watanni blyu kacal! Yasa daurin auran. Haka zallka dawainiyar kayan dakin Haneefa. Duk Yan-uwan Hajlya Sa'a ne suka dauke, kamar yadda aka saba. Ranar wata litinin. Musamman Muhseen ya dauki Umar suka shiga kasuwa, ba su fito ba, sai da ya kammala hada kayan lefansa. Domin zama su kayi suka ce a hado musu duk kayan da ake hadawa a lefe.Daga akwati har kayan cikin masu tsada ne. Da gani, ko ba'a tambaya ba, an san yayi kokari. Ya kuma kashe kudi kwarai da gaske, bayan dawowarsu, duk suna zube a saman kafet, a gajiye suke matuka da gaske. Muhseen na lumshe da idanunsa. Umar ya dan dube shi yace "M.U anyi me wuyar". Ya dan bude idonsa yana kallonsa yace "Haka ne. Allah dai yasa alheri za'a kulla". "Amen, ai gara dai ayi, da anyi shi kenan". Muhseen bai kara magana ba, illa idonsa daya maida, ya rufe shi kadai ya san abinda yake sakawa a ransa. Washe garin talata kuwa karfe uku a Jigawa tayi ma Muhseen, dakin Hajiya Goggo ya sa aka zube akwatinan lefen Haneefa. Haka zalika a dare ranar ya je gun Haneefa, ba wani dadewa yayi ba, domin ya bukaci ta gaya masa duk kudin da take bukata wanda za tayi