Page 52
amfani da su. Haneefa ta dube shi kasa-kasa tace "Naira dubu dari biyu sun isheni". Ido kawai Muhseen yasa mata, har ta gaji da kallonsa tace "Menene ka tsareni da ido? Ya yi kasa da idanunsa yace "Ina nazarin abinda za ki yi da dubu dari biyu ne. Haba Haneefa, ni ba wasa na tambayeki ba". "To tunda ba wasa ka tambayeni ba, sai ka ba ni abinda ka yi niyya." Ta fada cikin gintsewar fuska, cike da mamakin canjawar Haneefa, yasa hannu a aljihu ya fito da daurin dubu daya na dubu dari, ya mika mata. "Ga dubu dari nan". Ta amsa a wulakance, ba tare da tayi godiya ba, tamkar anyi mata biyan bashi. Ganin yau Haneefa a cikin wulakanci take, yasa tana karbar kudin. Ya kama kansa, ya tafi gida, zuciyarsa na cike da mamakin sabon canjin daya gani a wajen Haneefa. Yarinyar da kamar tsoron yin magana a gabansa take. Amma ya lura tunda bikinsu ya gabato, tamkar tana kokarin canja halinta, sai ta dinga yin abu garangatse! Koma dai menene, ita ce ta sani, domin dai babu 'ya macen da za ta wahalar da shi. Abinda yace kenan a ransa. Washegari yayi sallama da mutan jigawa, ya koma bakin aikinsa. Bayan Haj Gwaggo ta kara bashi maganin da ta kara karbo masa, ba don baya son ta gane baya amfani da maganin ba ai da ya daina karba. Ya koma ba tare da yayi sallama da Haneefa ba. Shirye- shiryen biki ya kankama gidan Sheik Sadisu yadda ka san baa taba aurar da jika ba, sai akan Muhseen, domin yadda ake ta shirye-shirye. Shi dai kam Muhseen ya barsu da shirye-shiryensu, domin a yadda ya tsara ma kansa ba zai kara zuwa Jigawa ba, sal bikin nasa. Rayuwa kenan, komai da lokacina. Muhseen da auransa ya tsaya ma kowa a rai, Kowa yasa masa ido, ya ki aure, ya zama katon tazuru. Sa'anninsa na daf! Da fara aurar da Ya'yansu mata, to shi ma Allah ya kawo lokacinsa na auran.