KALUBALE BOOK 1

Page 53

by @yargidanimam

Domin a ranar juma’a Misalin karfe biyu da rabi da minti shida na rana Muhseen Usman Jigawa ya shiga kwaryar manya, domin a wannan ranar ne ya tabbata angon Haneefa Jibrin, a sakamakon daura musu auran da aka yi a wannan ranar. Ango Muhseen shigar fararen kaya yayi, sama da kasa. Ita kanta fuskarsa walkiya da sheki take yi. Daurin auran nasa ya sami halartar dimbin jama'ar da ba za su ya lissafuwa ba, domin dai ko tawagar mutanan Sheik Sadisu sun fi gaban misali. Tun daga Malamai, Sarakuna da shugabanni. Muhseen ya tabbata dan lele, domin bikinsa ya fita daban, duk da ba'ayi wani badala ba, illa wa'azi da manyan Malamai suka gabatar. gwanin ban sha'awa. Jigawa ta san anyi bikin jikan Malam, wanda gidansu yayi tambarin sunan addini da Malanta, gidan da yayi fice akan hakan. Domin kwana bakwai ana wa'azi tare da karatun Alkur'ani. Anyi taro lafiya, an kuma watse lafiya. Amarya na dakin angonta. Sai fatan Allah ya ba da zama lafiya tare da zuri' a ta-gari. A daren ranar da Muhseen ya shiga dakin amaryarsa. Rikicewa yayi ya kasa tabuka komai, da ya wuce sun yi sallar nafila, kamar yadda Annabin rahama ya koyar da mu. Ya bata madara, ta sha, shi ma duk koyi da Annabin raham ne. Daga nan ya zame ya barta a dakinta, ya koma dakin da yake mallakinsa a gidan. Haneefa tayi ta jiran tsammanin dawowarsa, amma har barci ya kwasheta, bata ga dawowarsa ba. Washgari ma tun safe daya tashi cikin gidan Sheik Sadisu ya shiga yana dakin Hajiya Goggo, yana tambayarta gajiyar biki, bai bar dakinta ba, sai da aka kira sallar azahar. Tare da Sheik Sadisu su ka yi jam'i, bayan idarwarsu. Su biyu ne kadai a cikin masallacin, har Muhseen ya tashi shi ma zai fita. Sheik Sadisu ya dube shi yace "Ango, idan ka natsa anjima, ina son ka zo kai da martarka. Akwai maganganun da zan yi da ku". Muhseen ya amsa cikin fara'a "To Malam, muna nan tafe". Shi ma murmushi yayi. Daga nan ya fice kai tsaye gidansa ya shiga, tun kafin ya shiga falon.