KALUBALE BOOK 1

Page 54

by @yargidanimam

Yake sallama. Amma ba'a amsa ba, yayi tsammanin bata cikin falon ne, amma abinda ya ba shi mamaki, yana shiga falon ya tadda Haneefa kwance kan doguwar kujera, cikin tsararriyar kwalliyarta, hannunta na rike da rimot tana kallo har Muhseen ya shigo, ya sami wajen zama, ya zauna. Haneefa bata daga kai ta kalle shi ba. Ya dan dubeta yace "Kallo ki ke yi? Da alama gajiya, ta bi lafiya kenan". Ta dube shi shekeke tace "Dama ni ban gaji ba". Muhseen ya tsura mata ido, a zahiri yana ganin alamar tamkar ba Haneefar daya sani hace. Ya dauke kansa daga kallonta, sannan yace "Kin kunna (Heater) na ruman zafi a bandaki. Ko zan sami ruwan wanka." Ba tare da ta dube shi ba tace "Na kunna, amma bayan na yi nawa wankan. Na kashe. Ban sani ba ko akwai ragowa ko ya zama ruwan sanyi, amma kana iya zuwa ka kunna." Yasa mata ido sosal, cike da mamaki yace "Ke ba za ki iya zuwa ki kunna ba, ba aikinki bane? Ta dago ta dube shi tace "Aikina ne, amma kamar yadda kake kakarin ka manta da naka aikin, haka nì ma zan manta da nawa ailkin." Cike da mamaki Muhseen yace "Me ki ke nufi ne Haneefa? Ko ki na nufin ki ce daga kasancewarmu mata da miji, har na fara bata miki, har na fara shiga hakkinki? Haneefa ta gyada kai idanunta tsaye akan nasa tace "Eh, shiyasa kuma nake son na tabbatar maka da cewa idan da kafin ka auren, na shanye rashin nuna kauna a gareni, a yanzu da nake matsayin matarka, dole ne ka'aje wannan halin naka, matukar ka na kaunar mu yi zaman lafiya, zaman rufa ma juna asiri. Ya zama dole ka so-ni,, kamar yadda nake sonka, ka kuma damu da ni". Ta nisa tana ci-gaba da kallonsa "Kowane ango yana dokin amaryarsa tare da damuwa da kulawa da duk abinda zai faranta mata. Musamman a darennsu na farko, amma kai me ka yi a daren farkon naka? Tunda muka gabatar da nafila, ka fice ka barni, saboda rashin damuwa da ni, kuma tunda garin Allah ya waye, ban sa ka a ido ba, sal yanzu. Me kenan? To ina ba-ka shawarar idan haka zuciyarka ke raya maka, haka za ka zauna da ni. To ka yi gaggawar canja shawara, don ba zan dauki bakin cikin da namiji ba. Haka zalika idan har tunanina a kan