Page 55
ba ka so-na gaskiya ne, to ka tursasa ma kanka fara kaunata, shine kawai za ka ji dadin zama da ni. Kuma ina son ka sani, aurena da kai sunansa mutu ka raba. Mun yi kenan, sai mutuwa. Don haka ya rage ruwanka." Tsananin mamakin kalamanta, yasa Muhseen ya kasa koda kwakkwaran motsi, illa kansa daya sadda kasa, zuwa wani dogon lokaci ya tashi a sanyaye, ya shige dakinsa zaune yayi a saman gadonsa, yayi tagumi da hannun biyu. Abinda ya guda kenan tun farko, domin yana gudun irin wannan, tun yarinya na ganin mutuncinsa har ta kai ta daina gani. Yanzu ga shi nan daga yin aure jiya-jiyan nan, har ya fara haduwa da matsalar daya guda tun farko. Yanzu ya zai yi? Baya tunanin zai zama shashasha gidansa ya fi karfinsa. Baya tunanin ace yau matarsa ta fi karfinsa. To amma anya zai iya yi mata abinda take so? Anya zai iya sonta? Zai iya damuwa da ita? Tambayar dâ yake yima kansa kenan. Amma tsawon lokaci bai samo amsar tambayarsa ba, daga bisani ya aje tunanin komai, ya fada bandaki da ruwan sanyi, yayi wanka bayan ya gama kintsa kansa. Waje ya kara samu ya zauna har aka kira sallar la'asar. Ya daura alwalarsa, ya fice har yanzu Haneefa tana zaune tana kallo. Haka ya wuceta, ya fita zuwa masallaci, zuciyarsa cike da damuwa. Koda aka idar da sallar la'asar, cikin masallaci yayi zamansa yana karatun Kur'ani, bai gushe a cikin wannan halin ba, har magariba tayi. Nan ma bai fita ba. Sai da aka idar da sallar issha'i, sannan Muhseen ya koma gidansa. Wannan karon ma ko sannu da zuwa bai samu daga Haneefa ba. Shi ma kuma bai yi mata magana ba, sai daya gama duk abinda yake yi, sannan ya sameta daki a zaune. Ya dan dubeta, sannan yace "Malam na bukatar ganinmu yanzu". Ta amsa da "To". Ba tare da ta dube shi ba, ya wuce zuwa falo, yana cewa "Ina jiran fitowarki a falo". Bai ji amsar da ta ba shi ba, a dalilin har ma ya isa falon, yana tsaye yana jiran fitowarta. Lokaci kankani ta fito sanye da dogon hijabi har kasa, ya wuce gaba, tana binsa a baya, har cikin gidan Sheik Sadisu.