Page 56
Dakin Hajiya Goggo suka fara shiga. Tana ganinsu tare, ta shiga washe baki. Murna ce sisai a fuskarta. Ta kamo Haneefar ta
Zaunarv da ita kusa da ita tana fadin "Ni ba ni kishi, ba abinda zan jL, don na ganki tare da mijina." Haneefa tayi dariya tace "Dama ai ba'a san Mowa da kishi ba, tunda ta riga ta kama mijin", Tayi murmushi tace *Kin dai yarda da cewa nice Mowa? "Na yarda, don na san duk duniya, ba matar da zal so sama dake." Ta dubi Muhseen, wanda yayi shiru yana dubansu, tace "Wai haka Magajin Malam? Ya daga kansa yace "Babu shakka". Gaba daya suka yi dariya, daga nan Muhseen ya dubeta yace *Kiran Malam muka amsa Hajiya". Tace "Eh dama yanzun nan dana fito daga dakinsa, yake tambayata cewar kun shigo? Nace 'A'a ba ku karaso ba tukuna, sai ku tashi, na yi muku rakiya". Gaba daya suka tashi, suka nufi wajen Malam Sadisu. Suna tafe suna ba juna dariya har falon Sheik Sadisu, inda suka tadda shi Zaune. Duk kasa suka zube, banda Hajiya Goggo da ta sami kusa da tsohon mijinta ta lafe, tana dubansa cike da kauna. Sannan tace "Malam sun karaso". "To uwargida." Furucin nasa yasa kowa dariya, daga bisani duk suka sami natsuwa, sannan Sheik Sadisu ya kara gyara zaman gillashinsa dake fuskarsa ya fara Magana "Muhseen da Haneefa, ba don komai na bukaci ganinku ba, sai don na yi muku nasiha gami da jan hankalinku akan zaman aure". Ya gyara zamansa ya ci-gaba da cewa. "Kun ga zaman aure, abu ne ba na wasa ba. Aure sunna ce ta Annabin rahama, me karfi. Ya kuma ce duk wanda ya ki sunnarsa, to baya tare da shi. Duk ko wanda Annabi baya tare da shi. To ya zama tabbabe. A yanzu duk kun zama amanar juna. Muhseen ka na da ilimi, ka san komai, don haka ba ni da bukatar tunatar da kai hakkokin da suka rataya a wuyan ka na ma'aurata, amma abinda na sani ne, dole ne ka tsare mata ci da sha da tufatarwa da kuma sha'awarta. Haka zalika ya zama dole a gareka ka zama me kishin ¡yalinka, domin duk wanda baya kishin iyalinsa. To Allah ya haramta masa Jin kamshin aljanna. Balle ya shigeta, don haka ya zama dole