KALUBALE BOOK 1

Page 57

by @yargidanimam

ka kiyaye, ka ba matarka tarbiyya ta kwarai. Domin iyalinka abin kiwonka ne. Wanda za'a tambayeka yadda ka kiwata su a gaban dukkan halittun duniya. Matarka sirinka ce, ka kula da ita, ka hidimta mata, domin duk wanda ke kyautata ma iyalinsa. To kullum Allah zai dinga bude masa kofo fi na alheri a rayuwarsa . Haka zalika da ka bada sadaka a waje, gara ka zo ka taimaki matarka da abinda za ka bada sadakar, kada ka manta mace tana da daraja, tana da kima da martaba. Don haka duk abinda za ka yi, kada ka ce za ka wulakanta mace, komai kankantarta, ina fatan ka fahimci inda na dosa? Muhseen ya daga kansa, jikinsa a sanyaye yace "Na fahimta Malam" Daga nan ya waiwayi Haneefa. "Ke ma na san kin yi iliminki, wanda za ki iya gane muhimmancin miji a rayuwar 'ya mace. Mata Ajannarku ga mazajenku take, ko yaya mace ta daga harshenta akan mijinta, tana cikin tsinuwa da la'antar Ubangiji. Duk irin kuntatawar da mijin zai miki, matukar ki ka ce za ki rama. To sai kin sami zununbin daya ninka na shi. Don haka nake kira a gareki da ki yi biyayyar mijinki, domin ki fita ko ki tsira daga cikin matan da Annabin rahama ya gani a cikin wuta. Ki zama me boye sirin mijinki, domin duk matar da take bayyanar da sirrin mijinta. To tana cikin tsinuwar ubangiji, kin ga ko uwar ma da ta haifi mutum, idan ta tsine masa, fadama garari yake, balle Ubangijin daya halicceka. Don haka ki taimaki kanki Haneefa, ki yi zaman aure kamar yadda addini ya tanadar mana, Domin samun tsira". Yana nisawa. Hajiya Goggo ta amsa: "Kuma ina rokonku da ku yi Kokarin kawo kyakkyawan misali akan auranku, domin kada ku manta ku ne 'ya'ya na farko da aka fara hadin zumunta a Kansu Idan kuka yi taka tsan-tsan, sai ku kara dankon zumunci, idan kuka yi sakaci, ku watsa zumunci, wanda ba ma fata. Don haka don Allah ku zauna lafiya, ku taimakemu, ku hada kai. Muhseen ya dago a sanyaye yace "Mun gode kwarai da Gaske. Allah yayi mana jogara". Tace "Amin". Haneefa ma ta