Page 58
dago ta dubesu, sannan tace "Na gode". Daga nan bayan wasu yan mintoci hirarraki suka biyo baya, domin ba su bar gaban Malam ba, sai sha biyu saura na dare. Sannan suka yi sallama da su, suka nufi gidansu har suka kai, babu wanda yayi ma wani Magana. Wannan karon Haneefa ce a gaba. Muhseen na bin-ta a baya, jiki a sanyaye cikin tunanin magananun Malam. Suna shiga falo, kowa dakinsa ya wuce. Muhseen ya sami kusan mintoci goma zaune akan gadonsa, yayi tagumi, hannu biyu. Kwarai da gaske Sheik Sadisu duk abinda ya gaya musu gaskiya ne. Dole ya damu da matarsa. To amma matsalar daya ce, ya san zai ¡ya takura ma kansa ya damu da ita. Amma ba zai taba iya turasa ma kansa sonta ba, domin dai sam! Baya jinta a zuciyarta, bai jin zai iya sonta, sai dai matukar yana son ya sami zaman lafiya da ita, kuma yana son mutuncinsa ya dore. To dole ya damu da ita. Dole ya nuna mata hakan, batun sonta kuwa tunda bata da ikon ganin zuciyarsa, balle ta gane baya sonta, ai da sauki. Ya tashi ya shiga bandaki yayi wanka, ya kintsa kansa, ya fito sannu a hankali zuwa dakin matarsa. Dai-dai daya saura minti goma na dare. Yayi zaton zuwa wannan lokacin zai tadda Haneefa ta fara barci. Amma ga Mamakinsa tana zaune bakin gadonta, idanunta biyu, cikin taushin murya yace "Ba ki yi barci ba Haneefa?" Ta dago ta dube shi. Kayan jikinsa da kamshin da yake yi. Ya taimaka wajen kara mata sonsa da sha'awarsa, idonta kuri a kansa tace "Ban yi barci ba, domin ina son na tabbatar da cewa nasihar Malam ta shigeka, ko bata shigeka ba". Yay murmushi gami da zaunawa kusa da ita yace "Ta shigeni Haneefa, don haka ina fatan zamu sami zaman lafiya da fahimtar juna, domin ina sha'awar ace auren nan na mu ya zama abin alfaharin danginmu" Ta cika da fara'a tace "Ni ma ina fatan hakan". Ya dan tsareta da ido yace "Na zo tayaki barci ne, ko zai yuwu? “Abinda take son ji kenan, domin dai ta kosa ta fahimci abinda ke cikin auran, ta kosa ta fara dandanar abinda duk wata matar aure take dandana. Haka zalika ta kosa ta ji yadda abin yake, domin dai shekarunta ashirin da biyu, tana bukatar da namiji a rayuwarta, don haka tayi dan murmushi