Page 59
Tace "Zai yuwu mana" . Tsawon lokaci babu wanda ya kara Magana, domin dai zuciyar Muhseen ta fada sarkakiya da tunanin yadda zai sarrafa Haneefa a wannan daran. Alhalin bai san yadda abin yake ba, ya dai karanta a littafai. Amma duk shekarun nan nasa, bai taba kebewa da wata ya mace ba. Ya dan dubi Haneefa yace 'Ayi hakuri da ni domin ni ma sabon shiga ne, kamar yadda kike sabon shiga". Kunya ta dan kamata da maganarsa tayi kasa da kanta Daga bisani Muhseen ya aje tsoro da kunya, ya haye gadon Haneefa. Domin dai ya fahimci Haneefa a shirye take, don haka zai yi lya kokarinsa wajen faranta mata. Don haka abinda ya faru tsakanin Muhseen da Haneefar a wannan daren sirin ne, tsakanin ma’aurata wanda Allah ya haramta bayyana shi. Don haka ni dai abinda zan iya bayyanawa, shine Muhseen ya riski matarsa kamar yadda ko wane ango ke kwadayin , riskar matarsa. Ta rike budurcinta har gidan mijinta, maganar gaskiya hakan ya dasa ma Muhseen ganin mutuncinta da kwarjininta. Ya kuma sami kansa da yi mata godiya, mara iyaka ya kuma ji tabbas! Babu abinda ba zai iya yi mata ba, domin ta ji dadi, ita kanta Haneefa ta fahimci yadda ta sami wata daukaka da kwarjini ga Muhseen, yadda ya dinga yi mata godiya da yabonta. Yasa ta jì ta garau! Dan ciwurwukan da ta ji, sai ta ji gaba daya sun daina yì mata zafi. Ta sami kanta cilin farin ciki mara misaltuwa a wannan daran. Uku saura minti goma sha biyar Muhseen ya sauko daga kan gado ya shiga bandaki yayi wanka gami da dauro alwalarsa. Haneefa na kalionsa ya maida kayansa. Daga nan ya janyo sallaya ya haye, dai-dai tarfe uku da minti goma na dare. Daga nan ya ci- gaba da gabatar da sallar nafilarsa, tun Haneefa na kallonsa har barci ya kwasheta. Muhseen da Haneefa sun gabatar da amarcinsu kamar yadda kowane ma'aurata masu son junansu suke gabatanva, domin dai Muhseen ya takura ma kansa wajen nuna ma Haneefa shi ma fa yana kaunarta, domin dai shi kadai ya san gaskiyar zuciyarsa. Akalla sai da ya kwashe makonnì biyu a jigawa kafin ya koma wajen aikinsa a Kaduna.
Ku dakace ni
Daga taskar
Yar gidan Imam KALUBALE BOOK 1 Daga Habiba Abubakar Imam (Mrs Aliyu Mayere)
Bismillahir Rahma Nirrahim